Gwamnatin Kano ta yanke shawarar amincewa da buɗe makarantun boko 528 na jihar a ranar 10 ga watan Agusta.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Uamar Ganduje, ta amince da buɗe makarantun domin rubuta jarrabawar kammala karatun sakandire ta bana a sassan jihar.
Muhammad Sanusi Kiru, kwamishinan ilimi na jihar, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta.
Kwamishinan ya kuma umarci dukkan shugabannin makarantu da su fara shirye-shirye karbar ɗaliban makarantun kwana 'yan ajin shida a ranar 9 ga Agusta, yayin da na 'yan jeka-ka-dawo za su koma a ranar 10 ga watan Agusta.
Ganduje ya ƴanta firsunoni 43 Daga gidan yari
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/ganduje-ya-antar.html
An iyakance buɗe makarantun ga ɗaliban da ke ajin karshe masu shirye-shiryen zana jarrabawar kammala karatun sakandire.
A yayin haka ne gwamnatin ta ce za ta yi feshin magani a dukkan makarantun gwamnati da na masu zaman kansu 528 domin tabbatar da aminci a yayin zana jarrabawar kammala karatun sakandire wadda hukumar WAEC ke shiryawa.
Mista Kiru ya bayyana cewa Gwamna Ganduje ya umarcin ma'aikatar mahalli tayi feshin magani a makarantun da hakan zai tabbatar dalibai da kuma malamai sun kuma fagen fama cikin aminci.
- Haka kuma kwamishinan ya sanar da cewa, Ganduje ya umarci ma'aikatar lafiya ta jihar ta fara rarraba takunkumin rufe fuska, sunadarin tsaftace hannu (Sanitizer) da kuma sauran kayayyakin kariya daga kamuwa da cutar korona.
KARANTA KUMA:
GWAMNA ZULUM YA TONA ASIRIN WAƊANDA SUKE CIN AMANA A YAƙI DA TA'ADDANCIN BOKO HARAM
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/gwamna-zulum-ya-tona-asirin-waanda-suke.html
Baya ga kyautar ababen da ke dakile bazuwar cutar korona ga makarantun, Ganduje ya kuma ba da umarnin a yi wa dukkan dalibai da malamai a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu gwajin cutar korona kyauta.
Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Talata ne aka bada umarnin buɗe duk makarantun sakandire na gwamnatin tarayya 104 kamar yadda karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ba da sanarwa.
Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, yayin da ya kammala tattaunawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da ke fadin tarayya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong ya sanya wa hannu, ya yabi shugabannin makarantun dangane da tabbatar duk wani shiri na komawar ɗalibai a ranar Talata.
Tun a ranar 26 ga watan Maris ne Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe duk makarantun kasa sakamakon barkewar annobar korona, matakin da ya shafi makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.
No comments:
Post a Comment