Mutane 135 sun mutu 5,000 sun jikkata Sakamakon fashewar wasu sinadarai a Lebanon - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Wednesday, August 5, 2020

Mutane 135 sun mutu 5,000 sun jikkata Sakamakon fashewar wasu sinadarai a Lebanon

Mutane 135 sun mutu yayin da mutane 5,000 suka jikkata Sakamakon fashewar wasu sinadarai a Lebanon

Ministan Lafiya a Lebanon ya bayyana babu daÉ—ewa cewa mutanen da suka mutu sakamakon fashewar sinadarai ranar Talata sun zama 135 tare da jikkata wasu 5,000, a cewar kafar Al Manar TV.

Ministan yaÉ—a labarai ya sanar da saka dokar ta-É“aci ta tsawon mako biyu

Majalisar ministoci ta nemi jami'an tsaro da su tabbata ba su bari wani ya je wurin da fashewar ta faru ba a ranar Talata

Fiye da mutum 100 ne ba a san inda suke ba kuma ana tsaka da ayyukan ceto

Shugaban Ƙasa Michel Aoun ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon fashewar tan 2,750 na sinadarin ammonium nitrate - wanda ake haɗa takin zamani da shi - bayan an ajiye shi ba tare da kulawa ba a wani wurin ajiya.

Gobara ta yi barna a shalkwatar ECOWAS a Abuja
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/gobara-ta-yi-arna-shalkwatar-ecowas.html

No comments:

Post a Comment