Obaseki ya aikata laifin da ya kamata a tsigeshi - Tinubu ya ɓara
Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tsoma bakinsa cikin dambarwar siyasar dake gudana a majalisar dokokin jihar Edo.
Tinubu ya ɗaura laifin kafatanin abubuwan dake faruwa kan gwamnan jihar, Godwin Obaseki, inda ya ce ya ci wa demokradiyya mutunci.
A jawabin da ya wallafa daren jiya, Tinubu ya ce tsare ƙofar majalisar domin hana ƴan majalisa shiga a rantsar da su cin mutunci ne ga kundin tsarin mulkin ƙasa.
Ya bayyana cewa "Abubuwan da Gwamna Obaseki yayi a shekara ɗaya da ta shuɗe ko shakka babu ya cancanci a tsigeshi"
Ya ƙara da cewa duk da haka "wadannan yan majalisar ba suyi barazanar tsigeshi ba. Kawai manufarsu ita ce su gudanar da ayyukansu kamar yadda al'ummarsu suka buƙacesu."
A cewarshi, "Dalilin hana zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin jihar Edo aikinsu da doka ta buƙacesu, gwamna Obaseki ya yaudari al'ummar jiharsa kuma ya bayyana jahilcinsa ga kundin tsarin mulkin Najeriya a fili."
Ya ce a matsayin gwamna, ya kamata a ce Obaseki "ya sani fiye da gama garin mutane kafin hana majalisar dokokin jihar, amma yana buƙatar a koya masa darasi yanzu."
Ya kamata mulki ya koma yankin Kudu suyi shekara taƙwas -El Rufa'i
https://www.arewagist.com.ng/2020/08/gwamnan-jihar-kaduna-nasiru-el-rufai-ya.html?m=1
No comments:
Post a Comment