National Youth Investment Fund:
A lokacin da aka fara bada kyautar kuÉ—i na Youth Enterprise With Innovation in Nigeria (Youwin) a tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan da yawa daga cikin matasan basu san ma da shirin ba.
Wasu daga cikin waÉ—anda suka sani basu yarda cewa gwamnati za ta iya ba da kuÉ—i kyauta daga naira miliyan É—aya zuwa miliyan goma ba. Wasu kuma sai da suka ga mun samu sannan suka yarda cewa ana bayarwa.
Wannan shiri na matasa zalla shi ake kira da National Youth Investment Fund (NYIF) ko kuma Youth Bank. Kimanin kuÉ—i naira biliyan saba'in da biyar aka ware don matasa.
Samar da NYIF ba ƙaramin ci gaba bane a wannan ƙasar a daidai wannan lokaci, musamman idan akayi la'akari da cewa tun da aka kafa ƙasar nan ba'a taɓa samar da tsari kamar shi ba.
A wannan shirin na NYIF matasa kimanin dubu É—ari biyar ne za su ci gajiyar kuÉ—in daga shekera ta 2020 zuwa 2023.
An samar da wannan tsari don a tallafawa matasa wajen fara, gina wa da kuma bunƙasa sana'a da kuma gudanar da aiyukan hannu wanda ake amfani da fasaha da kuma basira.
Abin da za'a yarjewa wanda za su ci gajiyar shirin ya fara da mafi ƙaranci N250,000 zuwa N50 million. Mafi ƙarancin abinda za'a fitar a kowace shekara shi ne N25 billion tsawon shekaru uku.
A ƴan watannin da suka rage na wannan shekarar ta 2020 za'a buƙaci N12.5 billion don fara aiwatar da shirin.
Matasan da suka cancanta za su nemi wannan kuɗin ne daga ƙananan bankuna masu ba da rance (micro-credit banks) kusan guda ɗari da ashirin da biyar dake faɗin Nijeriya.
ÆŠanbar Da Matasan Za Su Sa Don Cin Gajiyar NYIF
1. Business Idea: Ka tabbatar ka yi nazari akan irin sana'a ko kasuwancin da za kayi, kafin ka ci gajiyar wannan tsari.
Wannan shi zai nuna cewa ka yi yunƙuri wajen tunanin me za kayi, kuma ka yi bincike a kan damarmaki da kuma ƙalubalen da ke cikin sana'ar da za ka fara ko kake yi.
2. Business Plan: Ka tabbatar ka shirya jadawalin fara kasuwanci wanda dole sai da shi ne za kaci gajiyar wannan tsari.
Shi business plan ɗin ka zai ƙunshi bayanai na yadda za ka gudanar da kasuwancin ka da kuma fasalin yadda za ka kasafta kuɗin da za a ba ka.
3. Business Registration: A duk wani tsari na ba da rance ko tallafi ko kuma sa hannun jari an fi É—aukar wanda yake da rajista ta kamfani, an fi É—aukar sa da muhimmanci akan wanda ba shi da ita.
Yin rijista ta kamfani na nuna cewa da gaske kake kuma har ka fara amfani da kuÉ—in ka don cimma burin ka na yin sana'a ko dogaro da kai.
Kana iya yin ƙaramar rajista amma in da hali kayi babbar. Za ka iya tuntuɓar masana akan abin da yafi dacewa.
4. TIN Number: Wannan lamba ta haraji na da muhimmanci ga wanda yayi ragista ta kamfani kuma yake fatan cin gajiyar tsarin gwamnati.
Samun ta zai sauƙaƙawa mai neman cin wannan gajiya na shirin NYIF.
5. Voters Card or National ID: Ka tabbatar kana da ɗaya daga cikin waɗannan katuna domin duk cancantar ka ba za ka samu damar cin gajiyar tsarin ba in har ba ka da katin zaɓe ko na zama ɗan ƙasa.
6. BVN Validation: Ka tabbatar kana da lamba ta BVN kuma ba ka da matsala ta saɓanin suna ko kwanan watan haihuwa.
Idan har ka cika waÉ—annan sharuÉ—É—a to da yardar Allah za ka samu damar cin gajiyar wannan tsari na bawa matasa jari.
Source
Comr.Alkamatu Hussaini Abdulkadir
+2348130075757
Thursday, August 13, 2020
New
Yadda za ka Sami tallafin da gwamnatin tarayya za ta bayar na Naira Bilyan 75
About Bahaushiyanews.com
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
Tattalin Arziki
Tags
Labarai,
Tallafi,
Tattalin Arziki
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment