Gwamnatin Filato ta tabbatar da wawashe wuraren ajiyar kayan abincin Tallafin Korona
Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da rahotannin wawashe É—akunan ajiyar kayan tallafin annobar korona da dubban mutane suka yi a Jos, babban birnin jihar.
Sai dai ta ce ba gaskiya bane batun da ake yaɗawa cewa ɓoye kayayyakin tayi, tana mai cewa zanga-zangar EndSars ce ta tilasta dakatar da raba wa mabuƙata.
Cikin wata sanarwa da Kwamishinan YaÉ—a Labarai Dan Manjang ya fitar a yau Asabar, an yashe wuraren ajiyar abinci na Jos da Bukuru ranar Asabar 24 ga Oktoba.
An ga dubban mutane a wasu bidiyo daban-daban da suka karaÉ—e shafukan sada zumunta suna É—ibar kayayyaki daga wurin ajiyar abinci a Jos.
"Gwamnati ta yi tur da wannan aiki sannan tana jaddada cewa ba É“oye su tayi ba," in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa a ranar 16 ga Oktoba Ministar Ma'aikatar Agaji, Cigaban Al'umma da Kare Afkuwar Bala'i, Sadiya Umar Farouk, da Ministar Mata Dame Paullen Tallen, suka kai kayan tare da ma'aikatan da za su raba su.
No comments:
Post a Comment