Jawaban gwamnan Legas Sanwo-Olu kan harbin Masu Zanga-zanga a Lekki
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi bayani ga jama'ar Legas kai tsaye a kafafen yaÉ—a labarai na talabijin na jihar a safiyar Laraba.
Gwamnan jihar ya bayyana cewa bai da ikon juya sojoji ko kuma ba su umarnin suyi wani abu, ya kuma ɓukaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da bincike kan abin da ya faru.
Gwamnan dai ya bayar da umarnin dakatar da duk wasu abubuwa na gudanarwa na gwamnatin jihar amma banda jami'an tsaro, haka kuma ya umarci rage tsawon tutocin da ke a gine-ginen gwamnatin na kwanaki uku domin nuna goyon bayan zanga-zangar.
Gwamnan kuma ya bayar da haƙuri kan duk wani abin da ya faru kuma yayi kira ga matasan jihar da su rungumi zaman lafiya.
Jawabin na gwamnan na zuwa ne dai bayan rikice-rikice daban-daban da aka samu a jihar ta Legas tun daga yammacin jiya Talata har zuwa yau Laraba.
No comments:
Post a Comment