Shekara 120 rabon da asamu adadin ƙuri'ar da aka jefa bana a Amurka
Sama da Amurkawa miliyan 160 suka fito jefa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, wannan adadi shi ne mafi yawa na 'yan ƙasar da suka fito jefa ƙuri'a a shekaru 120 da suka gabata, kamar yadda aka ƙididdige yayin zaɓen.
A 1900, Shugaban Amurka ɗan Jam'iyyar Republican William McKinley ya kayar da abokin karawarsa na Jam'iyyar Democrat William Jennings Bryan inda aka samu kashi 73.7 cikin 100 na masu zaɓe da suka fito jefa ƙuir'a.
A wannan shekarar kuma kashi 66.9 cikin 100 na masu zaɓe ne suka fito don jefa ƙuri'a.
A bana dai, masu sa ido kan zaɓe sun yi hasashen za a samu mutane da yawa da za su fito jefa ƙuri'a tun bayan da aka sanar da cewa wasu za su yi zaɓe ta hanyar aika wasiƙa ta akwatin gidan waya sakamakon annobar korona.
No comments:
Post a Comment