Duk wanda ba a saka lambar katin shaidar zama ɗan kasa ba a rijistar layin sa, za a doɗe layin – Pantami
Ministan Sadarwa, Ali Pantami ya gargadi ƴan Najeriya masu layin waya cewa kowa ya garzaya ya gyara layin sa na kira ta hanyar saka lambar shaidar katin zama ɗan kasa ko kuma a doɗe layin ya dai na aiki kwata-kwata.
Hakan ya biyo bayan ganawar da ministan yayi da shugabannin kamfanonin sadarwa na Najeriya.
” Wannan sako ne gare ku masu amfani da layukan waya, kowa yaje ya gyara layin sa ta hanyar saka lambar katin shaidar zama ɗan kasa nan da makonni biyu, wato zuwa 30 ga watan Disamba, idan ba haka ba za a doɗe layin.
Sanarwar ta ce duk wanda bai saka wannan lamba ba za a doɗe layin sa kwata-kwata, za ta dai na aiki. Layukan sun hada da masu amfani da MTN, Etisalat, Glo da Airtel.
Idan ba a manta ba Ma’aikatar sadarwar a makon jiya ta fidda wata sanarwa dake umartar kamfanonin sadarwa, MTN, Glo, Airtel, 9Mobile kada su sake yi wa wani sabon layi rajista.
Ma’aikatar ta ce ta yi haka ne domin ta iya kammala tantance layukan da aka riga aka yi wa rajista a kasar nan da samun cikakken bayanan su wato cikakken bayannan wanda ke da mallakin duk wani layi.
Ma’aikatar ta ce duk kamfamin da aka samu ya karya wannan doka ya kuka da kansa, domin har lasisin sa gwamnati za ta kwace.
Domin siyan DATA ta MTN wadda take yin wata daya 1GB Kan 350 yi magana ta WhatsApp https://wa.me/c/2348107747229
No comments:
Post a Comment