Abubuwa Biyar (5) da Zaka/kiyi Domin Mallake Zuciyar Budurwa/Saurayinki
Yau na danyi Nazari kadan inda na leka sashen su Nura Nakowa domin yau na kawo muku wasu hanyoyi da mutum zaibi a matsayinsa na wayayye domin ya sace zuciyar budurwarsa ba tare da farga ba, ko kuma shi ta sace tasa.
1. Abu na farko shine dolene masoya su mayar da junansu manyan abokai mafi kusanci, matukar baka zama babban aboki ga budurwarka ba ko ki zama babban aboki ga saurayinki to babu shakka akwai sauran aiki.
Ki dauki fadin Malam Umar M. Sharif da yake cewa “Zan Rayu dake zan mutu dake, Abadan dani dani dake zamu zauna” “Idan babu ke nima ba’a ganni ba, duk inda kike nan wurin amin marhaba…” ba wai ka daukeshi a wake ba a’a ka aikata shi a aikace, ka nuna kana matukar damuwa da ita, haka kema.
2. Ka zamo mai magana daya, kada ka/ki yiwa masa/ta karya duk abinda zaka fada ya zamo gaskiya, ya zama idan kika fada masa magana to baya shakku kada ki sake ki baiwa saurayinki damar kina fada masa magana yana yin shakku akanki, ko kana fada mata tana karyataka, matukar aka samu wannan kofar to hakika babu ranar dai-daituwa.
3. Girmama Juna, ya zama kina bashi girmansa, Namiji ko yaushe shi babbane kina ce masa Ranka ya dade, Yallabai da sunayen na Musamman na girmamawa, kaikuma namiji dolene ka dinga lallabata domin ita mace kullum ’yar shagwabace tana son ka dinga nuna mata kulawa sosai.
4. Ka Fahimceta ta Fahimceka, da yawa yanzu ana samun wannan matsalar mata basu tsayawa su fahimci dabi’un samarinsu ballantana su san ta yaya zasu mu’amalancesu, haka suma mazan basu fahimceta ba balle a samu dai-daito.
Yana da kyau ki fahimci abubuwan da yake so da wanda bayaso, shima kuma ya fahimci hakan akanki, hakan zai taimaka muku wajen kaucewa samun matsala, kuma indai kikayiwa namiji hakan to ba zai taba iya rabuwa dakeba, don wallahi ko yayi wata budurwar sai ya dawo.
5. Ki dinga bashi lokaci, ba wai ko yaushe baki da lokacinsa ba, haka shima, amman kada lokacin ya dinga wuce kima, ki dinga kiransa a waya (missed call) shima ya dinga kiranki, kar kuyi wasa da ZAFAFAN KALAMAI …
6. Ki dinga sanar dashi idan zakiyi wani abun wannan zaisa shima ya dinga kula dake akai-akai.
7. Kada ki dinga yawan rokonsa, kai kuma namiji tilasne ka dinga yi mata IHSANI wato kyautatawa tunda Hausawa sunce ai Kulawama Yabawace.
8. Ke dashi ku dinga yiwa juna Uzri, sannan ku dinga baiwa juna hakuri a duk sanda daya yayiwa day aba dai-dai ba.
Fatan Soyayya mai Dorewa.
Basheer Sharfadin Kano
Feb, 2019
No comments:
Post a Comment