ABUNDA MUSULUNCI YACE AKAN RANAR MAZINATA/MASOYA [VALENTINE DAY]
.
BY: Ibrahim Nasir (Sultan)
.
GABATARWA: Faridah Bintu Salis (Bintus~sunnah)
.
FITOWA TA DAYA
.
Dukkan yabo da godia sun tabbata ga ALLAH mai girma da daukaka wanda yake cewa: "idan kabi mafi yawan wadanda ke bayan kasa zasu 6atar da kai daga hanyar ALLAH, basa bibiyar komai face zato...." [6:116], Tsira da amincin ALLAH su qara tabbata ga Manzon ALLAH, Bawan ALLAH, Shugaban jiya mai gidan yau, cikamakin tsiran gobe, Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wasallam) wanda yake cewa: "wallahi zaku bibiyi sawun wadanda suka gabace ku sawu bayan sawu, koda kuwa zasu shiga ramin damo zaku bisu. Sai muka (sahabbai) ce: Ya Rasulullah Kana nufin yahudu da nasara? Sai yace: idan basu ba suwa kenan?" [Bukhari da Muslim] mutanen gidansa sahabbansa da dukkan wanda ya biyo bayansa da imani da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
.
"Yan'uwa Musulmai Manzon ALLAH (sallallahu alaihi wasallam) Yana cewa: "wanda yayi kama da wata Al'immah yana daga cikinsu" [Imam Ahmad da Abu dawud]
.
•ASALIN RANAR MAZINATA/MASOYA [VALENTINE DAY] .....
.
A Tarihi, kiristoci sunyi qoqarin kawo asalin wannan rana, amma asalinsa ba bikin kiristoci bane. Tarihi ya nuna asalinsa daga wani irin biki nea maguzanci da rumawa keyi wanda suke qiransa da suna LUPERCALIS wanda ake yi ranar 14/15 ga watan Feburairu (February) wanda suke qira da suna bikin gane yabanya ta hanyar tara samari da 'yan mata tsararrakin juna bayan an gama caca wajen gane wacce zata haihu sa qadda ba zata haihu ba. Wannan shine asalin saint valentine a lokacin da suke qiransa da suna Lupercalis.
.
Bayan zuwan kiristoci qasar Roman sai suka dauki wannan dabi'a ta maguzanci suka masa kwaskwarima ta hanyar mayar masa da sunan daya daga cikin waliyyi irin nasu mai suna SAINT VALENTINE, daya ne daga cikin manyan Malaman cocinsu, sanadiyyar haka ne Fafaroma Gracious a shekara ta 469 yake cewa: shi Valentine wanda ya rayu a qarni na 3 yayi abun kirki saboda a zamaninsa akwai wani azzalumin sarki wanda hatsaniya ta shiga tsakaninsa da mai gidansa, saboda haka a matsayinsa na mai wa'azi sai ya shiga tsakaninsu domin ya sasanta tsakaninsu, wannan sai ya jawo soyayya tsakanin 'yar maigidan da Valentine.
.
Lokacin da sarakuna suka samu labari sai ya kai ga abu yayi tsanani har an yanke masa hukuncin kisa, sai wannan yarinyar ta samu labari kuma hankalinta ya tashi amma sai yake fada mata kada ta damu ita tashi ce. Saboda wannan matsayi ne yakai cocin Roman Catholic suke daukaka shi a matrayin wanda yayi mutuwar shahada.
.
Daga wannan rana ne Fafaroma Gracious ya bada sanarwar cewa daga yau bikin ranar Lupercalis an chanja ya koma ranar Masoya [SAINT VALENTINE DAY]. daga nan dai ba a rabu da Bukar ba an haifi Abu (Ma'ana ba a rabu da d'a ba anzo an haifi uba) saboda asalin abun maguzanci ne ya koma kiristanci.
.
Wannan ya sanya duk lokacin da wannan rana ta zagayo a qasashen turai zaka samu samari da 'yan mata sun samu gonaki sun kwanta tsirara. Kuma har yau muma kwatankwacin abubuwan da ke faruwa kenan ga samarinmu da 'yan mata a jami'o'I da sauram manyan makarantu.
.
Tunda wannan shine tarihin biki to ko shakka babu dole ne mu koma ga Alqur'ani da Sunnah, kuma muyi la'akari da fadin ALLAH (SWT): "Yaku wadanda sukayi imani kada ku riqi Yahudawa da Nasara a matsayin maji6anta, sashen su maji6inci ne ga sashe, kuma wanda ya ji6ince su daga gare ku to lallai yana cikinsu, lallai ALLAH baya shiryar da mutane azzalumai. Sai kaga wadanda acikin zukatansu akwai cuta, suna tseren gaggawa acikinsu...." [suratul Ali-imran 3:28]
.
Kamar yadda Manzon ALLAH (sallallahu alaihi wasallam) ya tabbatar cewa dukkan wanda yayi kamanceceniya da wasu mutane to yana cikin su.
.
Mu hadu a FITOWA TA 2 Inshaa ALLAH.
.
#Repost.
#HaramValentineDay.
#FaridahBintuSalis.
#Bintussunnah.
Wednesday, February 13, 2019
New
ABUNDA MUSULUNCI YACE AKAN RANAR MAZINATA/MASOYA [VALENTINE DAY]
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
FAGEN ADDINI
Tags
FAGEN ADDINI
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment