DAGE ZABE DA RAININ HANKALIN APC
Kamar yadda aka tsammana, a qarshe dai Hukumar INEC ta dage zaben da aka shiryo cewa za a yi yau Asabar. Dagewar ba abin mamaki ba ne, domin dama wata kafa ta hango haka bisa ga dalilan da suka bayyana cewa Buhari ba zai ci zabe ba. Abin mamakin shi ne hanzarin da bangaren watsa labarai na APC ya gabatar na dora wa PDP alhakin dagewar ta bakin Festus Keyamo. Wannan tsagwaron rainin hankalin 'yan Nijeriya ne!
Shirin safiyar yau na BBC ya kawo rahoton cewa, Shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Mahmud Yakubu, rai bace ya fito don shaida wa manema labarai labarin dage zaben jiya da tsakar dare. Shin me wannan yake nufi?
Idan an ce ba ya nufin komai, to ga tambaya, wane sakaci ne ya hana Hukumar Zabe, tun a shekaranjiya, tuttura "election materials"? Ba ta da isassun kudi ne, ko kuwa zaben ya zo mata bagtatan ne ba ta shirya masa ba?
A lokacin Jonathan, in ba a manta ba, irin haka ta faru amma ba a qurarren lokaci haka ba, shin wa ya dora alhakin a kan APC a wancan lokaci? Ashe ba Dasuqi (tsohon mai ba Jonathan shawara a harkar tsaro) ne ya jajirce sai an dage ba saboda dalilan rashin tabbacin tsaro? Amma shin tsaron ne da gaske?
Idan shugaban qasa bai yarda a dage zabe ba, shin don Allah INEC za ta iya? Wane ne ya dauki shugaban INEC din? Wai me ya sa 'yan APC ke raina hankalin jama'a ne?
Muhammad Bin Ibrahim
16/02/2019
Saturday, February 16, 2019
New
DAGE ZABE DA RAININ HANKALIN APC
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
GIST
Tags
GIST
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment