Dage Zabe: Hukumar Zabe Tayi Abun Kunya.
Daga Mahmoud Assalafy Yola
Shin yaya INEC zata yi da wadanda suka koma gida daga wurare masu nisa don zabe? yaya mata za suyi da kunu da zobo da suka hada don sayarwa ranan zabe? yaya 'yan bautan kasa (NYSC) da suka kwana a wurin zabe a sarari babu dakuna za suyi? Yaya jami'an tsaro da hukumomin sa'ido da suka kwana a garuruwa don aikin zabe zasuyi?
A fahimta ta, INEC ta yi babban kuskure duk da biliyoyin kudi da ta nema gwamnatin tarayya ta ware mata saboda ayyukan zabe.Hotuna sun bayyana yanda ma'aikatan zabe 'yan bautan kasa suke kwana a kasa a sarari a wuraren zabe saboda sakacin INEC.
Wannan abun kunya ne ga kasar Nijeriya a dion duniya. INEC tana da shekaru uku don shirya kowani zabe amma kullum sai an daga yayin da hakan dole ya shafi mutane da dama.
Duk da haka ba za mu yi kasa a guiwa ba zamu fito mako mai zuwa. Allah ya sanya hakan shine mafi alkhairi.
Friday, February 15, 2019
New
[[Dage Zabe]] Hukumar Zabe Tayi Abun Kunya.
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
GIST
Tags
GIST
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment