_MAHAIFA SUNA SAMUN GAFARA TA HANYAR ADDUAR 'YA'YANSU ACIKIN QABARINSU - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, February 12, 2019

_MAHAIFA SUNA SAMUN GAFARA TA HANYAR ADDUAR 'YA'YANSU ACIKIN QABARINSU

*_MAHAIFA SUNA SAMUN GAFARA TA HANYAR ADDUAR 'YA'YANSU ACIKIN QABARINSU_*.

Yana daga cikin hakkin mahaifan mu akan mu, yawaita yi masu addua da nema masu gafara a wajan Allah,har ma wadan su malamai suna ganin Allah baya amsar adduar bawa har sai idan yana yi ma mahaifansa addua.

Daga Abi Hurairata رضي الله عنه yana cewa:
"Manzon Allah ﷺ yace:"
*(Lallai Allah yana daukaka matsayi da daraajar mutum a gidan Aljanna, Sai mutumin yayi tambaya,yace:"Ya Allah wannan karin matsayin daga ina??" Sai ace dashi,dalilin neman gafarar da 'ya yanka suke makane)*
@صححه الألباني-صحيح الجامع الصغير- (1617).

Awani Hadisin Manzon Allah ﷺ yace:
*(Idan dan Adam ya mutu, dukkan aiyukansa ladansu ya kare inbanda aiyuka guda ukku,Sadaka mai gudana,ilimin da ka koyar ake amfanuwa dashi,da kuma 'Da na kwarai wanda zai riqa yi maka addua)*
@الألباني-صحيح الجامع الصغير

Yana cikin alamar mutum shi mutumin kirkine idan yana yawaita yin addua ga mahaifansa kamar yadda hadisi ya tabbatar.

شيخ الإسلام ابن تيمية-رحمه الله-:
Yana cewa:
_*"Bawa na kwarai bazai gushe ba yana nemawa mahaifansa gafara ba,har sai Allah yayi masu gafara, sannan Allah ya daukaka matsayinsu a cikin Aljanna"*_
@شرح الوصية الصغرى(صـ131).

Yan uwa dan Allah mu yawaita addua ga mahaifan mu tare da nema masu gafara.

Wannan shine wasiyata agaremu baki daya.

*اللهم_إغفر_لنا_ولوالدينا_وللمسلمين والمسلمات_الأحياء_منهم والأموات🌺أمين*

No comments:

Post a Comment