MENENE T-POINT???
T-point wani application ne dake zuwa a cikin wayoyin mutane musamman wayoyi masu upgraded version wato manyan version.
Shi wannan T-point shine abinda kake gani akan screen din wayarka wadda idan ka danna tsakiyan shi sai kaga wasu options guda biyar (5) sun fito.
An kirkiri wannan application dinne domin ya saukakewa mutane wasu abubuwa, kenan ya zama kamar shortcut ne shi.
Wannan option da T-point yake dasu sune:
1. Apps shortcut
2. Screenshot
3. Close current app
4. Go to desktop
5. Show minimize apps.
Bayan ka bude wannan T-point din, wato ya nuno options 5, Idan kanaso kaga manyan Apps dinka kamar Facebook, WhatsApp da saransu sai ka danna 1.
Idan kuma screenshot kakeso kayi sai ka danna na 2, Idan kanaso a rufe App da kake kai sai ka danna na 3, idan kanaso kaje kan desktop direct sai ka danna na 4 idan kuma kanaso kaga apps da ka minimizing sai ka danna 5.
Da wadannan options 5 zaka iya sarrafa wayarka ba tare da kasha wahala ba.
Idan baya nunawa a screen dinka, ka shiga cikin wayarka, ka duba ko akwai app mai suna T-point sai kaje ka selecting on, idan ko babu kenan version din wayarka bazai iya daukawa ba.
Wasu suna korafin cewa abin yana fito musu akan screen kuma basu so, to yadda zaka cire wannan abun shine, ka shiga wayarka zakaga App mai suna T-point sai ka bude shi ka selecting off, shikenan.
Kalli hoton dake tattare da wannan rubutun domin ganin T-point din.
Kullun kuyita zuwa wannan shafin domin samun bayanai masu amfani.
#Abu Abdirrahman Kaltungo
#CEO Arewagist.com.ng
5 February, 2019
Tuesday, February 5, 2019
New
Menene T-point a cikin waya, kuma yaya ake aiki dashi???
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
ILIMI
Tags
ILIMI
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment