NAMIJIN GORO DA AMFANONINSA GA LAFIYAR DAN-ADAM. - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, February 7, 2019

NAMIJIN GORO DA AMFANONINSA GA LAFIYAR DAN-ADAM.

NAMIJIN GORO DA AMFANONINSA GA LAFIYAR DAN-ADAM.

Daga: Nura Ibrahim Khalil, Zaria

(1) YANA KASHE DAFIN MACIJI:
Namijin goro yana kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to a bashi namijin goro guda daya ya ci, insha'Allahu nan take zai kashe dafin cizon macijin.

(2) YANA KASHE MACIJI:
Ana shanya namijin goro ya bushe sai a daka, a barbada a wajen da ba a so macijin ya shiga, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take zai mutu.

(3) YANA KASHE GUBA:
Duk wanda ya sha wata guba da gan-gan ko bisa kuskure, a basu namijin goro kwara daya ya cinye, insha'Allah zai amayar da gubar da ya sha.

(4)YANA FITAR DA DUK WANI CUTA:
Ana yayyanka namijin goro a jika a rika sha, insha'Allah duk wata gubar da ke jikin mutum za ta fita.

(5)YANA KARA KARFI:
Ana cin namijin goro saboda da karin karfi ga masu iyalai 'yan mintuna Karin a je ga iyalan.

(6)YANA MAGANIN CIWON GABABUWA:
Cin Namijin goro na magance matsalar ciwon gabobi, kamar yawan gullewa da zugi, yana kuma rage kowane irin radadin azaba.

(7)YANA MAGANIN (STD)
Yawan cin namijin goro na kashe kwayoyin cutar da ake dauka wajen saduwa wato STD.

(8)YANA MAGANIN HUNHU:
Cin namijin goro goro na kara lafiyar hunhun dan-Adam.

(9)YANA GINA GARKUWAR JIKI:
Namijin goro na da kaso mai yawa na sinadarin 'antioxidant' Wanda ke da muhimmancin gaske wajen yakar kwayoyin cututtuka da kuma sake gina garkuwar jikin dan-Adam.

(10) YANA MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURO:
Namijin goro rigakafi ne daga kamuwa da zazzabin cizon sauro.

(11)YANA KARE IDANU DAGA MAKANTA:
Cin namijin goro na kare idamu daga makancewa.

(12)YANA KASHE GYAMBON-CIKI
Mai wannan larura idan yana cin namijin goro to! insha'Allah zai warke.

Na bada wadannan bayanai ne saboda Allah (T) da nufin Allah ya kai ladan ga ruhin mata ta Marigayiya. Hajara Idris, 'ya ta, Marigayiya. Amina Nura Khalil da kuma da na Marigayiya. Hasan Nura Khalil.

No comments:

Post a Comment