PANTAMI YA KADDAMAR WA YAN NIGERIA MANHAJAR INTERNET MAI SUNA DIGITAL NIGERIA PORTAL AND MOBILE APP - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Monday, September 28, 2020

PANTAMI YA KADDAMAR WA YAN NIGERIA MANHAJAR INTERNET MAI SUNA DIGITAL NIGERIA PORTAL AND MOBILE APP

 


Mai girma Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani Dr Isa Ali Pantami ya kaddamar da sabuwar manhajar Internet da ta wayar salula ga 'yan Nigeria wanda aka yiwa take da "DIGITAL NIGERIA PORTAL AND MOBILE APP" a Ranar Litinin 28-9-2020 da misalin karfe daya na rana 


Ministan ya gabatar da wannan tsarin ne domin samar da dama tare da garabasa ga 'yan Nigeria wajen koyan sana'o'i iri daban-daban na zamani, da samun ayyukan yi cikin sauki, kuma an tsarashi yadda kowa zai iya koya da kanshi ta hanyar gani a video da rubutu, wannan tsarin yana da matukar mahimmanci ga 'yan Nigeria.


Wannan tsari yana da saukin fahimta da kuma saukin amfani ga mai aiki da shi, sannan ba sai kana da data a wayar ka ko computer zaka iya shiga tsarin ba, tsarin an raba shi kaso uku:


1. Digital Nigeria

2. NITDA Academy.

3. IBM Digital For Africa

Kowani tsari yana da mahimmanci, kuma za'a baka certificate bayan kammala training din, ga yadda tsarin yake da yadda za'ayi amfani da manhajar da kuma amfanin su ga 'yan Nigeria.


(1) "DIGITAL NIGERIA''

Shi wannan tsarin yana da fannoni da yawa a tare dashi, zaka koyi sanin me nene computer da yadda ake sarrafa ta da kuma sanin manhajoji da computer ke dauke dasu, sannan ta yaya zaka sarrafa su dan ka nemi kudi dasu?


Misali akwai tsari na masu koyo wadanda basu san computer ba kamar haka:


DIGITAL SKILLS:

(a) Yadda zakayi aiki da computer.

(b) Yadda zaka samu bayanai ta Internet.

(c) Yadda zaka bayar da kuma yada bayanai ta yanar gizo.

(d) Yadda zaka kiyaye kanka daga sharrin 'yan damfara a yanar gizo.

(e) Yadda zaka kir-kiri wani abu da computer.

(f) Yadda zaka kula da manhajar ka a computer.

(g) Yadda za kayi ammani da manhajar Microsoft office.


Sannan akwai tsari na wadanda sun fara koyon computer, da sanin yanar gizo tsarin su yana nan kamar haka;

INTERMIDIATE DIGITAL SKILLS:

(a) Yadda zaka kirkiri manhajar computer

(b) Yadda za kayi manhajar HTML da CSS

(c) Yadda hakayi manahaja mai nazari da kanshi

(d) Yadda zakayi ammani java script

(e) Yadda zaka kir-kiri Manhaja


Da kuma tsarin wadanda sukayi nisa da sanin computer da yanar gizo harma da kirkire-kirkiren manhaja da computer, suma ga tsarin su kamar haka;


ADVANCE DIGITAL SKILLS:

(a) Yadda za kayi amfani da Data science analytical

(b) Yadda za kayi ammani da HTMAL 5

(c) Yadda za kayi amfani da node.Js

(d) Yadda zaka koyi Netwoking

(e) Yadda zaka koyi kir-kiran manhajar kwamfuta da na wayar hannu

(f) Yadda zaka koyi aiki duk wani nau'i na kumfuta da manhajar sa.

(g) Yadda zakayi kasuwa da komfuta ta hanyar yanar gizo

(h) Yadda zaka tallata kasuwar ka ta hanyar yanar gizo

(i) Yadda zaka nemi masu sayan kayan ka ta hayar yanar gizo

(j) Yadda zaka bayar da gudummswa ga gwamnati ta yanar gizo.

(k) Yadda zaka dauki ma'aikatan ka ta yanar kizo.

(l) yadda zaka nemi aiki ta yanar gizo.


Yadda Zaka Samu Rancen Kudin Kasuwanci na tallafi Daga Gwamnatin Nigeria

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/yadda-zaka-samu-rancen-kudin-kasuwanci.html?m=1


(2) "NITDA ACADEMY"

Shi kuma wannan yana da tsari kashi uku wanda masu bangaren zasu amfana dasu, kamar haka;

(a) MDAs Training:- yana da courses da dama.

(b) Students Training:- yanada courses nashi da dama dasuka shafi yan makaranta

(c) General Training:- wannan ya shafi kowa da kowa


(3) "IBM DIGITAL FOR AFRICA"

Wannan tsari ne wanda kamfanin Amurka ke koyarwa domin fahimtar manhajar zamani a Afrika, suma gasu kamar haka;

(a) Yadda zaka koyi yin manhaja da artificia intelligent.

(b) Yadda zaka koyi yin manhaja da data science.

(c) Yadda zaka koyi yin manhaja da internet of things.

(d) Yadda zaka koyi yin manhaja da machine learning.

(e) Yadda zaka koyi yin manhaja da blockchain.

(f) Yadda zaka koyi yin manhaja ta hanyar github


Amfanin su ga 'yan Najeria:

1. Samun ilimin computer kyauta

2. Samun aikinyi cikin sauki

3. Koyon sana' o'in Zamani cikin sauki kyauta

4. Sanin surrun 'yan damfara (yahoo boys).

5. Samun arziki cikin sauki da sauri.

6. Samar da kudin shiga.

7. Bunkasa tattalin arzikin kasa.

8. Rage aiyukan ta'addanci.


Sannan ana so a fahimci cewar ko wane tsari yana da 'ya'ya a kasa da shi, sannan kuma in kuka gama kowani tsari za'a baku certificate.


Domin shiga tsarin a shiga cikin wannan adireshin na yanar gizo ayi rijista.


https://www.digitalnigeria.gov.ng

Ko https://academy.nitda.gov.ng


Idan an shiga cikin website site din zai nuna yadda kowa zai shigar da bayanansa, abi abubuwan a hankali za'a fahimce su, kuma ya kasance kowa yana da Email wanda yake aiki da kuma lambar waya.


Kada a manta wannan tsarin yana bukatan wanda yake rike da babbar waya, a kalla wayar da take iya bude manhajar WhatsApp, kuma tana iya bude application na Opera da Google Chrome, sai kuma wanda yake da computer, zai fi samun saukin koyon abubuwan, 'yan Arewa kada kuyi wasa, kowa ya shiga ya nema don ya amfana, wanda bai gane ba ya tambayi na kusa dashi masani akan fasahar yanar gizo don karin bayani.


Wannan aiki ne da zai gudana kyauta karkashin jagorancin Mai girma  Ministan Sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami da taimakon hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani ta Nigeria NITDA Nigeria karkashin jagorancin Babban Darakta Janar Malam Kashif Inuwa Abdullahi bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan kudurin da yake da nashi na rage yawan 'yan Nigeria masu fama da talauci tare da habbaka tattalin arzikin Nigeria.


Yau ne kowa zai iya fara neman tallafin naira bilyan 75 da Gwamnatin Nigeria zata bayar

https://www.arewagist.com.ng/2020/09/yadda-zaka-sami-tallafin-da-za-bayar-na.html?m=1



No comments:

Post a Comment