*INGANTATTUN MATAKAN TARBIYYAN YARA WANDA MASANA HALAYYAN DAN ADAM SUKA NAQALTO*
1. In kaga yara suna yawan son yin qarya to, da alamu kana yawan tsananta musu horo in sukayi laifine.
2. In ba’a koya wa yara sanin muhimmancin fadin gaskiya tare da musu ahuwa ko rangwame yayinda sukayi laifi to, zasu iya girma a qangare.
3. In yara suka kasance a qasqance ko yawan raina kansu to, mai yiwuwa kana yawan zaginsu ko musu fadane kawai a lokacinda sukayi laifi, amma ba ka yawaita qarfafa musu gwiwa wajen ganin sun kasance yara na gari.
4. In kaga yara sun gaza wajen kwatar ma kansu ‘yanci a wajen 'yan uwansu yara to, da alamu kana yawaita hukuntasu a bainar jama’a ne tun suna qanana.
5. In kaga yara na yawan daukan abinda ba nasuba to, mai yiwuwa baka cika basu za6i bane a duk lokacinda zaka saya musu wani abu.
6. In yaranka suka kasance matsorata a ko da yaushe to, mai yiwuwa kana yawan taimaka musune maimakon ka riqa bari tasu ta ficcesu kan abinda bai fi qarfinsuba ko wasu al’amuransu na yau da kullum wanda bai taka kara ya karyaba.
7. In kaga yara basuda tausayi ko girmama na gaba dasu to, mai yiwuwa kana yawaita tsawata musune kullum maimakon yi musu magana a tsanake.
8. In kaga yara na da saurin fushi to, da alamu ka fi sanya ido ne a duk lokacinda sukayi ba daidaiba amma in sukayi abin kirki sai ka kau da kanka kaman baka ganiba ballantana ka yaba musu.
9. In kaga yara sun cika qyashi da son kai to, mai yiwuwa kana yabonsune kawai a lokacinda suka kammala wani abu ko wani aikinda aka sanyasu amma ba ka yaba musu a duk lokacinda sukayi yunqurin aikata wani abu ko da basu kammala shiba.
10. In kaga yara na yawaita damunka ko yawan sa ka magana to, da alamu baka yawan kula da al'amuransune ko yawan jan su a jikine. Yara suna jin dadi suga iyaye ko wani babba ya nitsu tare da muhimmantar da abinda sukeyi.
11. In kaga yara ba sa yawan bin umurninka to, da alamu kana yawaita tsoratasune in sukayi laifi ba tare da ka tabbatar ka basu horonda ka ambata din ba.
12. In kaga yaro na 6oye maka abinda yakeyi to, kana yawaita hanasu yin abune ba tare da basu dalilin hanasunba, yanada kyau kayiwa yaro bayanin illan abinda yake qoqarin yi wanda ba mai kyauba.
13. In kaga yaro na mayar maka da maganan to, tabbatar cewa ya ga kanayi wa wasune a gabansa, sai shima ya koya. Don haka, a kiyaye don haka na yawan faruwa tsakanin ma'aurata in akwai dan rashin jituwa.
14. In kaga yara na jin maganan wasu amma basa jin magananka to, da alamu kana saurin yanke musu hanzari ko saurin yanke hukuncine da zaran sunyi wani abu.
Yana da kyau iyaye su riqa sauraran bayanan yaransu tare da musu adalci da kuma rangwame wajen hukunci.
15. In kaga yaro ya bijire maka to, ya lura kana amfani ne ko muhimmantar da abinda mutane ke gaya maka game dasu; ba tare da ka bincika ainihin abinda ya farun ba.
Da fata iyaye zasu kiyaye wadannan muhimman nazari da masana halayyan dan adam suka naqalto don samun kyakkyawan tarbiyyan yaranmu.
Da fata iyaye zasu cigaba da sanya ‘ya’yansu cikin addu’a a duk yanayinda suka lura yaran na aikata halayyan da bai daceba a maimakon yin kuka dasu ko tofin alatsine musamman a gaban yaran ko a bainar jama'a.
In yaro yayi laifi, ka zaunar dashi ka masa bayanin illan abinda yayin tare da tsoratar dashi ko bashi horo mafi dacewa in bai bariba.
Allah ya albarkaci zuriyarmu gaba daya.
(Daukar nauyi Center for Advocacy of the Right of a Child CARAC)
Cibiyar bayar da shawarwari kan tarbiyyan yara
08033022168
No comments:
Post a Comment