HAKKOKI GUDA 10 NA MAHAIFA BAYAN RASUWARSU - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, April 4, 2019

HAKKOKI GUDA 10 NA MAHAIFA BAYAN RASUWARSU

HAKKOKI GUDA 10 NA MAHAIFA BAYAN RASUWARSU

    Darasi na farko-(1)

Yana cikin biyayya da kyautatawa mahaifa da hakkinsu akan mu bayan Allah ya karbi rayuwarsu;

*1-Nema masu gafara da yi masu Istighfari*

Ya kai dan uwana wajibine mu yawaita nemawa mahaifanmu gafara a wajan Allah alokacin da suke raye sannan mu kara nema masu gafara da yi masu istighfari kowane lokaci mai yawa bayan mutuwarsu.
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Lallai Allah yana daukaka Daraja da matsayin mutum Salihi acikin aljanna,sai bawan yace;Ya Allah daga inane nake samun karin wannan daukaka,sai Allah yace masa;Saboda ISTIGHFARIN ya'yanka)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ

*2-Yi masu addu'a*

Wajibine ga kowane Da na kwarai ya riqa yima mahaifansa addu'a duk lokacin da zai roki Allah,kuma ya kara dagewa da wannan addu'ar a garesu bayan rasuwars.

Yana daga cikin alamar kai na kirkine a sameka kana yawaita addua ga mahaifanka.
Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Idan Dan-Adam ya rasu,ladar aiyukansa sun yanke sai guda ukku kadai;Sadakar da yayi mai gudana,ko ilimin da ya koyar ake amfanuwa da shi,da Da nakwarai da zai riqa yi masa addu'a)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ. 

*3-Biya masu dukkan basuka da yake kansu*

Bashi kala biyune kamar yanda Manzon Allah SAW ya bayyana;
-Bashin mafi girma bashin Allah

-Bashi mai girma bashin dake tsakanin mutum da mutum.

Dukkan wadan nan basukan hakkine na mahaifanmu akanmu da mu sauke masu bayan rasuwarsu.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Ran mumini idan ta mutu ana kangeta daga isa zuwa ga rahama har sai an biya mata bashin da yake kanta)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ. 

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Wanda yayi mutuwar Shahada ana gafarta masa dukkan komai inbanda bashin da yake kansa)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ

Annabi SAW yace;
*(.........Bashin Allah shine yafi chanchanta da abiya masa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ. 

*4-Cikisa bakancensu da alqawulansu na alkhairi*

Wajibine a biya masu bakancensu da alkawulansu na alkhairi,kamar Azumi ko aikin hajji ko Umara ko wani daga cikin alkawula na alkhairi.

*5-Biya masu hakkin kaffara da yake kansu*

Kamar kaffarar kisan kai bisa kuskure ko kaffara ta rantsuwa ko wanin wannan to shima yana cikin hakkin mahaifa akan ya'yansu da su biya masu bayan rasuwarsu.

Wata mata tayi bakancen zakayi azumi na wata guda,amma bata samu damar cikawa ba har ta rasu,sai yan uwanta sukazo wajan Manzon Allah SAW suka bashi labari,sai yace;
*(Shin da abana binta bashi zaku biya mata??* sai sukace Eh ya Manzon Allah,sai yace;
*(To bashin Allah shi yafi chanchanta da abiya)*
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ. 

Da matar nan da ta tambaye Manzon Allah SAW cewa;-
"Mahaifiyata ta rasu ana binta azumin wata guda,sai yace;
*(Ki rama mata)*
@ﺃﺑﻮ ﺩﻭﺩﺍ. 

Manzon Allah SAW yace;
*(Dukkan wanda ya rasu ana binsa bashin azumi to yan uwansa su biya masa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ 

     Allah ne mafi Sani.

*Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah*

No comments:

Post a Comment