*_RASHIN KARANTA ALQURANI A GIDA YA KAWO KUNCI DA RASHIN WALWALA A GIDAN_*
Karatun alqurani yana janyo albarka da kwanciyar hankali da nishadi da saukar rahama da nutsuwa alokacin da ake karanta shi da wajan da ake karanta shi.
Kamar yadda Annabi s.a.w yake cewa:
*(......Babu wadan su mutane da zasu hadu a wani daki daga cikin dakunan Allah,suna karanta littafin Allah kuma suna yin darasinsa a tsakaninsu face rahama ta sauka agareshu kuma nutsuwa da lullubeshi kuma Mala'iku sun kewaye su......)*.
@Muslim
Rashin karatun alqurani da rashin kokarin sanin ma'anoninsa shine dushen dukkan wani kunci da rashin samun damuwa a rayuwa,babu alkhairi ga wanda baya karanta alqurani babu alkhairi agidan da ba'a karanta alquran.
Gidan da ba'a karanta alqurani ya zama tasha ta shaidhanu da aljannu da dukkan wani kunchi na rayuwa.
Daga Abi Hurairata R.A yana cewa:
*"Lallai gida yana samun nutsuwa da jin dadi kuma Mala'iku suna halartasa kuma Shaidhanu suna nisantarsa kuma alkhairi yana yawaita acikinsa idan ana yawaita karatun alqurani acikinsa.Kuma gida yana samun kunci da rashin nishadi da walwala da jin dadi ga masu gidan, kuma Mala'iku suna nisantar gida kuma shaidhanu su mamaye gidan,kuma Alkhairi yayi karanci acikinsa sharrin ya yawaita,idan ba'a yawan karatun alqurani acikinsa"*.
@ﺻﺤﻴﺢ ، ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺪﺍﺭﻣﻲّ ( ٣٣٥٢ )].
Allah ka bamu ikon raya gidajenmu da karatun alqurani mai girma da sunnar Annabi s.a.w a ilmance da aikace.
No comments:
Post a Comment