SHEKARUN DA MATA SUKE FARA YIN HAILA DA KUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, April 11, 2019

SHEKARUN DA MATA SUKE FARA YIN HAILA DA KUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA

SHEKARUN DA MATA SUKE FARA YIN HAILA DA KUMA SHEKARUN DA SUKE DAINAWA


 Tambaya :
Malam ban wuce shekaru goma sha daya ba a duniya, amma na shiga bandaki sai na ga wani jini ya fito min, har ya fara jika karamin wandona, to malam shin wannan jinin haila ne ko kuma na cuta ne ? don na ga kamar shekaruna ba su kai na yi jinin haila ba, Allah ya yi maka albaka a rayuwa. 

Amsa :
To 'yar'uwa yawancin mata suna fara yin haila ne daga shekara 12-50 amma wani lokacin mace tana iya yin haila kafin shekara 12 ko kuma bayan shekara 50 wannan ya danganci yanayinta da kuma Wurin da take zaune. Malamai sun yi sabani : shin akwai wata shekara
ta musamman da mace take fara haila ko kuma take dainawa, ta yadda jinin da ya sameta kafin wannan ko bayan wannan shekarun ba za'a kira shi jinin haila ba?

Darimi -Allah ya yi masa rahama- ya ce bayan ya ambaci sabanin da aka yi: (Wannan duk kuskure ne a wajena), domin abin lura shi ne samuwar jinin, don haka duk lokacin da aka samu jinin a cikin kowacce shekara ne ya wajaba a sanya shi
ya zama haila" Wannan abin da Darimi ya fada shi ne daidai saboda Allah da manzonsa sun rataya hukunce- hukuncen jinin haila ne da samuwarsa, ba su
kuma iyakance wasu shekaru na musamman ba, kamar yadda aya ta :222 a suratul bakara take nuni zuwa hakan, wannan yake nuna mana iyakance shi da lokaci na musamman yana bukatar dalili na daga litttafin Allah ko daga sunnar manzonsa, ba’a kuma samu ba.
Saboda haka jinin da kika gani sunansa jinin haila, saboda kamar yadda malamai suka fada duk jinin da ya fito daga gaban mace sunansa jinin haila mutukar ba'a samu wani dalili da yake nuna cewa na cuta ne ba . Allah ne mafi sani Don neman karin bayani duba : Dima'uddabi'iyya shafi na : 6

*Amsawa*

*Dr Jamilu Yusuf Zarewa.*

10-04-2014

No comments:

Post a Comment