[[KA KARANTA]] ME KA SANI GAME DA JAMI'AR BUK DAKE KANO??? - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Thursday, July 4, 2019

[[KA KARANTA]] ME KA SANI GAME DA JAMI'AR BUK DAKE KANO???

AREWA STUDENTS AND ORIENTATION FORUM🎓

 No. 003 - 04th July, 2019(BUK)

      "MAKARANTUNMU"

Bayero University Kano Chancellor; His Royal Majesty King Alfred, papaprieye diete spiff.

Bayero University Kano vice Chancellor: Muhammad Yahuza Bello.

Buk Tanada Campuses Guda Biyu 2 Old site Da New site.

Old Site Address; No 3011 Kabuga Gwarzo Road Kano.


New site address;No. 3011 Dambare Gwarzo Road Kano.

Yawan Daliban Da Ake Dauka A shekara; Aduk shekara Jami'ar Bayero University tana dailukar sabbin Dalibai Under Graduate Kusan 10,000.

Yawan Dalibai; 29,777

Yawan Staffs; 3,323(Malamai)

Departmental Cut Off Marks Gashi Kamar Yadda Secretary General Ismail Saleesu Ali Yarubuta;

•Ko kanada labarin Jami'ar Bayeron dake Kanon dabon Nigeria ta fitar da Cut Off point dinta ?
•Shin Ya kamata Nayi Changing Course daga Jami'ar ta Bayero zuwa wata duk da kuwa Naci 180-185 ?
Jiya da rana ne Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Bayeron dake kanon dabon Nigeria ta fitar da Cut Off Point din ta, a wata takarda da ta samu sa hannun rajistarar Jami'ar wato Hajia Fatima Binta Muhammad.
A cikin takardar an bayyana 180 a matsayin maki mafi karanci da jami'ar take bukata Wanda Shine zai baka damar zana jarabawar su ta cikin gida wace ake kira da Post-UTME. Saidai ba kowane tsangaya (Faculty ) bane zasu iya baka gurbin karatu a jami'ar ba Dan kanada maki 180 a Jamb dinka. Akwai wasu tsangayoyi da jami'ar ta ware tace dole sai kaci maki da yakai 220.
Tsangayoyin kuwa sune:-
1• Clinical Sciences (MBBS)
2• Dentistry
3• Pharmaceutical Sciences
Haka kuma akwai wasu tsangayoyin da Jami'ar tace dole sai kaci makin da baiyi kasa da 200 ba, tsangayoyin sune:-
1• Allied Health Sciences
2• Law
3• Communication (amma a wannan tsangayar Mass communication ne kawai ake bukatar 200, sauran departments din da suke karkashin faculty din na Communication duka maki 180 suke bukata)
• Ni naci maki 180 kuma faculty dina 180 suke bukata, ni kuma naci maki 200 nima kuma 200 din suke bukata, ni kuma naci 220 ne, kuma daman 220 din Faculty na yake bukata, shin mu chanja Jami'ar ta Bayero Mu koma wata kokuwa mu bar shi ?
Ehh to, kai tsaye bazamuce mutum ya chanja ba, to amma dai ya danganta ne. Misali ka nemi MBBS sai kaci maki 220 a Jamb dinka, Yes, according to the University ka cancanta a baka gurbin karatu amma kuma abunda zaka duba shine: course ne da yakeda Competition.


Atakaice dai ba saina cika Ku da surutu ba, idan haka ta faru dakai to ka auna Course din ka gani, kai da kanka ma zaka gane idan zaka samu ko akasin haka.

Domin samun cikakken bayani ko Neman shawara akan ya kamata ka canja Course dinka, koma Jami'ar dungurungum sai Ku tuntubi daya daga cikin wadannan lambobin kamar Haka:-
08038485677
08033388750
Dangane da masu DE (Direct Entry ) kuma wadanda basu siya DE din ba Jamb sukayi, sai kuma aka samu akasi basuci Jamb din ba, ko kuma sun siya DE din, kuma sun siya Jamb duka a tare, shima dai sai basuci Jamb din ba, to zasu iya daukaka matsayin Jamb din nasu zuwa DE (Upgrading) kuma zasuyi haka ne ba tare da biyan wani kudi ba daga hukumar ta Jamb, saidai kawai kudin aikin da mai Cafe din yayi masu.
Saidai hukumar ta Jamb tana gargadin dalibai cewa idan ka canja sau daya to bazaka samu damar dawowa dashi jamb din ba, wannan Shine.


•Ranar da za,a fara rajistar da kuma Jarabawar
Rajistar ta Post-UTME ko kuma Screening exercise din zata fara ne daga ranar litinin takwas ga wata (8/07/2019) kuma za,a rufe ne a ranar Juma'a biyu ga watan Augusta (02/08/2019) shikuma Printing na Acknowledgment Slip zaikai karshe ne a ranar sha daya ga watan Augusta din (11/08/2019) inda kuma za,ayi Screening din ko jarabawar a ranar sha bakwai ga watan Augusta (17/08/2019).
Allah ya kaimu ya bawa mai rabo Sa,a.

Masha Allah Dahaka Muka kawo Karshen Program din Buk saura kuma wata Jamiar.

Marubuci: Abdulkadir Anas Malumfashi (07035764366)

No comments:

Post a Comment