*LABARAI A TAKAICE*
*Yanzu haka tuni gorunan ruwan zamzam dubu 51,699 sun iso Najeriya don mikawa kowanne Alhaji ko Hajiya da zarar isowa gida a filayen jiragen sama.*
*Sanarwa daga babbar jami'ar labarun alhazan Najeriya Fatima Sanda Usara ta ce an dau matakan ne na taho da zamzam din ga alhazai don hana cusa ruwan a cikin jaka da ya saba da dokokin zirga-zirgar jirage.*
*Hukumar alhazan Najeriya ta ce kamfanonin jirage biyu na Fly-nas da Max na cigaba da dawo da alhazan a kashi na 3 na karshe kuma kusan in ban da alhazai kimanin 70, duk alhazan sun samu ziyarar Madina.*
*Wani tsarin shi ne na tabbatar da nauyin babbar jaka kilogram 32 da kuma karama kilogram 8 ga alhazan don kaucewa rage kayan alhazan a filin jirgi musamman wadanda kan saba ka'ida ta hanyar jidar fiye da jakar hannu daya lokacin dawowa gida.*
*Zuwa yanzu sawun jirage 17 ya dawo da fiye da alhazai 7,647.*
*Kotun sauraron karar zabe na jihar Kogi a Najeriya, ya soke zaben dan majalisar dattawa da ya yi suna Dino Melaye da umurtar gudanar da sabon zabe a kwana 90 nan gaba.*
*Kotun ta yanke hukuncin ne biyo bayan korafin da tsohon abokin hamaiyar Melaye wato Smart Adeyemi ya shigar da ke zargin an tabka magudi a zaben. A baya dai Melaye ya taba tsallake zaben yi ma sa kiranye don rashin fitowar jama'a.*
*Akwai dai tsama tsakanin Melaye da gwamnan jihar Yahaya Bello wanda ya sa Melaye ke harin neman tikitin takarar gwamnan jihar a watan nuwamba karkashin jam'iyyar PDP.*
*Zuwa rubuta wannan labari, ba mu samu labarin ko Melaye wanda ya sha arangama da tsohon babban sufeton 'yan sanda Ibrahim Idris, ya daukaka kara ne ko kuwa a'a ba.*
*Sultan na Sokoto Muhammad Sa'ad Abubakar ya ce sarakuna za su cigaba da kasancewa a shirye don zaman lafiyar kasa da mara baya ga manufofin gwamnati. Sultan din na magana ne a lokacin da ya jagoranci tawagar sarakunan arewacin Najeriya da su ka gana da shugaba Buhari a fadar Aso Rock.*
*Jagoran sarakunan ya yabawa gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun don dagewa kan tattaunawa da dukkan sassa don samun jituwa daga illar tabarbarewar tsaro. Shugaba Buhari ya bukaci sarakunan su tallafawa 'yan sanda da goge war su wajen hulda da jama'a daga tushe don samun bayanai sirri na inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.*
*Sarakunan dai daya bayan daya sun yi ta musabaha da shugaban inda kafafen yanar gizo na 'yan arewa su ka fi maida hankali kan musabahar Sarkin Kano Sunusi Lamido da shugaba Buhari*
*Takaddamar jirgin ruwan Iran na dakon mai "ADRIAN DARYA" da ya dandana rikewa a Gibralter, ta kara tsami inda Amurka ke zuba ido don tabbatar da ba wata kasa da ta amince da karbar jirgin.*
*Da alamun wannan kalubale ya sanya jirgin sauya hanya inda yanzu ya nuna madakatar sa tashar MESRIN ce ta Turkiyya. Amurka dai na kara matsa lamba kan takunkumin hana Iran cinikayyar fetur da sauran kasashe bayan watsi da yarjejeniyar makaman kare dangi ta 2015.*
*Masana sun ce ba lalle ne jirgin da ke tafiya yanzu haka a tekun MEDITIRENIYA ta kudancin kasar Sicily na nufin isa MESRIN ba ne.*
*Ibrahim Baba Suleiman*
*Jibwis Media & Publicity*
*24-Dhul Hijjah-1440*
*25-August-2019*
Sunday, August 25, 2019
New
[[KARANTA]] LABARAI A TAKAICE NA YAU LAHADI 25 AUGUST 2019
About Dan Arewa
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
GIST
Tags
ENLIGHTENMENT,
GIST
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment