Ministan Noma zai Ciwo bashin Dala Bilyan 1.2 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Friday, May 15, 2020

Ministan Noma zai Ciwo bashin Dala Bilyan 1.2

Majalisar Zartaswa ta amimce a ciwo bashin dala bilyan 1.2 domin wadata harkar noma da manoma da kayan aikin gona.

Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan kammala taron Majalisar Zartarwa da aka yi ranar Laraba tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan taro da aka gudanar ta tsarin fasahar sadarwar Internet na talbijin ta kai-tsaye, yayin da kowane Minista ke halartar taron daga ofishin sa, amma kowa yana kallon juna.

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ce ta bada shawarar gudanar dashi ba tare da Ministocin sun hadu wuri daya ba, saboda tsoron kamuwa da cutar Coronavirus.

Sabo Nanono bai yi karin haske ba dangane da yadda za a ciwo bashin ba, Amma kwanan nan Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za tafi maida hankali ne ga ciwo bashi a cikin gida, maimakon a rika dogaro da kasashen waje, saboda barnar da cutar Coronavirus ta yi wa duniya.

Nanono ya bayyana cewa kananan hukumomi 632 ne za su ci moriyar bashin.

Minista Nanono ya kara da cewa, “a yau Ma’aikatar Gona data Harkokin Kudade sun mika roko domin a amince a ciwo bashin dala bilyan 1.2.

“ An yi haka domin kananan hukumomi 632 da kuma kananan masana’antun harkokin noma su samu bunkasa da kayan noma.

“Wannan zai kasance wani sauyin da zai zama gagarimin shirin da ba a taba ganin kamar sa ba.

Anasa bangaren, Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi, ya ce an amince a sai wa Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa  ciwo bashin naira milyan 683 wanda za a sayo  manyan Galla gallan  motoci guda 19.

“Wannan ne karo na farko da Hukumar NPA za tayi motoci a cikin shekaru hudu cur. Shi ya sa aka amince ba tare da wani ka-ce-na-ce ba.

“Ba motocin alfarma na shiga ba ne. Dukkan su samfurin Toyota Hilux ne domin karakainar aiki

No comments:

Post a Comment