Sabbin mutane 51 sun kamu da cutar covid-19 a jigawa
Kwamishinan ya ce a ranar laraba an Sami karin mutane 23 Wadanda sakamakon su ya Nuna suna dauke da wannan cuta, sannan Kuma yace cikin samfurin da aka Kai kaduna na Almajiran da suka dawo daga jahar Kano 28 suna dauke da wannan cuta.
Ayanzu mutane 169 ne ke dauke da cutar ta covid-19 a jigawa.
Ya ce fiye da Rabin mutanen da suke dauke da wannan cuta Almajiran da suka dawo ne daga jahar Kano.
Kwamishinan ya Kara da cewa Babban abin farin ciki shine akasarin masu dauke da cutar suna cikin hayyacin su, in Banda Mutane 2 zuwa 3 da alamu ke nuna cewa suna fuskantar zafin cutar, ya yin da su Kuma Almajiran da aka kwadasu Basu kamu da cutar ba aka salleme su zuwa mafi yawagidajensu.
Wanda mafi yawan Almajirai 630 da Gwamnatin Kano da mayarwa jigawa an kusa gama Gane matsayin lafiyar su, illa gwajin kadan da ake dakon sakamakon su.
Kwamishinan ya ce mutane 28 daga cikin mutane 51 da suka kamu Almajiran da suka dawo daga Kano ne, ya yin da Mutane 23 Kuma mutane daga jama'a gari ne da suka kamu da cutar ta hanyar mu'amala da Wadanda suka kamu da cutar.
Inda yace mutane 14 daga dutse suke,Sai wasu daga Ringing da birnin kudu da Kuma gwaram.
Ya ce akwai jami'an lafiya da Dana da suka kamu da cutar, Wanda yahada da Likitoci da Ma'aikatan jinya.
No comments:
Post a Comment