Buhari ya ce kucigaba Da Hakuri Tabbas Ana cikin Matsi
Muhammadu Buhari ya bukaci Musulmai su kasance cikin karfin gwuiwa duk da halin da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta zo dashi.
Shugaban ya bayyana hakane a cikin sakon da na barka da Sallah da ya aikewa ‘yan Najeriya ta hannun me magana da yawunsa,Garba Shehu, kamar yanda ya bayyan aranar Asabar.
Shugaban yace ba abune me sauki ba yin azumi ba tare da Sallar Taraweeh ba da kuma Tafsir ba, yace amma hakan ya zama dole saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.
Yace yana kira ga masu hali daga ciki suci gaba da taimakawa wanda basu da shi dan a samu a gudu tare a tsira tare.
Yace yana yabawa da sadaukarwar da musulmai da Kiristoci sukayi na hakura da taron ibada saboda wannan cuta.
Yace yana sane da hali matsin da Mutane ke ciki bisa wannan matakai da aka dauka.
Musamman masu kasuwanci da suka hakura da kasuwancinsu.
Yace babu gwamnatin da dagan gan zata dauki irin wadannan matakai masu tsauri akan ‘yan kasar ta saidai idan ya zama dole.
A karshe shugaba Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya fatan Allah ya kawo musu saukin halin matsin da suke ciki sannan kuma yace yana musu barka da Sallah.

No comments:
Post a Comment