KAMFANIN RABA WUTAR LANTARKI YA BAIWA GWAMNATIN JIGAWA TALLAFIN KAYAN ABINCI
Kamfanin raba wutar lantarki na jihohin Kano Kaduna da Jigawa KEDCO ya yabawa gwamnatin jihar jigawa bisa matakan data dauka na yaki da cutar covid 19.
Manajan Daraktan Kamfanin Dr Jamilu Isyaku Gwamna ya bayyana haka a lokacin da yake mika kayayyakin tallafi ga gwamna Muhammad Badaru Abubakar a gidan gwamnati.
Yace kamfanin KEDCO ya bada tallafin ne domin ragewa alummar jihar Jigawa radadin da suka fuskanta a sakamakon annobare cutar covid 19.
Dr Jamilu Gwamna wanda ya sami wakilcin daya daga cikin manyan jami'an kamfanin Mr Bujai Kamara yace ya zama wajibi a hada hannu wuri guda domin yaki da cutar coronavirus.
Ya kara da cewa kamfanin ya yanke shawarar bada gudunmawar ne sakamakon alakar dake akwai a tsakanin gwamnatin Jigawa da kamfanin tare da jaddada kudirin kamfanin na ganin alumma suna samin wutar lantarki akai akai domin debewa alumma kewa a lokacin zaman gida.
A jawabinsa bayan karbar kayayyakin tallafi gwamna Badaru Abubakar ya nuna farin cikinsa da irin tallafin da kamfanin ya baiwa Jigawa a irin wannan yanayi.
Kayayyakin da kamfanin ya bayar sun hadar da bahunan shinkafa dubu daya da galan dari na man gyada da kuma chak din kudi na naira miliyan biyu.




No comments:
Post a Comment