An sallami mutane 222 daga cikin mutane 283 da suka harbu da cutar coronavirus, bayan sun sami lafiya a inda gwamnati ta dage dukkannin dokar kulle da hana cin kasuwannin sati sati a Jigawa.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne, ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai a gidan gwamnati, inda Yace dage dokar ya biyo bayan raguwar wadanda suke kamuwa da cutar a jihar.
Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yace duk da an bude kasuwanni, akwai bukatar mutane su kiyaye da shawarwarin da kwararru a fannin lafiya suka bayar, domin hana yaduwar cutar.
Yace kin kiyayewa da wadannan shawarwari zai sa gwamnati ta sake rufe duk kasuwar da aka samu da saba dokar.
Gwamnan ya cigaba da cewar ya zuwa yanzu jihar Jigawa ta yiwa mutane dubu biyu da sittin gwajin cutar Coronavirus inda aka sami mutane 283 suna dauke da cutar, yayinda wasu 8 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Daganan ya sanar da karbar karin almajirai bakwai daga jihar Adamawa, wanda tuni aka musu gwaji kuma basa dauke da cutar, dan haka gwamnati ta mika su ga iyayensu.
No comments:
Post a Comment