Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dattawa, sunan Jastis Monica Dongban-Mensem,
Bisa lamunin da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa shugaba Buhari, yana neman amincewar majalisar wajen nadin Jastis Monica, a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu ne, ya wallafa sanarwar hakan a kan shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2020.
Haka kuma shugaban kasar ya tabbatar da wannan sanarwa da kansa a sakon da wallafa kan shafinsa na dandalin sada zumunta na Twitter a Yammacin ranar Litinin.
Kamar yadda lamarin ya zamto al'ada, hukumar shari'ar kasa, ta shawarci shugaban kasa Buhari akan nadin Jastis Dongban-Mensem a matsayin sabuwar shugabar kotun daukaka kara a kasar.
A halin yanzu Jastis Dongban-Mensem babbar mai shari'a ce a kotun daukaka kara.
Hakazalika ita ce mai rikon kwarya ta shugabancin kotun daukaka kara ta kasar nan.
No comments:
Post a Comment