Babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da karar da kungiyar dattawan Kano karkashin jagorancin tsohon dan takarar kujeran shugaban kasa, Alhaji Bashir Tofa, ta shigar kan sabbin Masarautun Kano a gwamnatin jihar ta kirkiro.
Kungiyar ta dattawan Kanon ta bukaci kotun ta rusa sabbin Masarautun biyar saboda hakan ya sabawa doka.
Alkalin kotun, N.S Umar ya yi watsi da karar ne bayan Antoni Janar na jihar Kano, Ibrahim Muktar, ya kalubalanci hurumin Alhaji Bashir Tofa na shigar da karar.
Haka zalika an rusa karar saboda yin hakan na iya tayar da tarzoma a jihar.
Kotu ta Yi watsi da karar da tsohon Sarkin Kano Mallam Muhammadu ya shigar
Hadiman gwamnan jihar Kano kan labarai, Salihu Tanko Yakassai da Abubakar Aminu Ibrahim ne, sukaa bayyana hakan a shafinsu na Facebook da safiyar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020.
Sunce "A jiya litinin 8 ga watan June, wata kotu karkashin jagorancin Mai Shariah N.S Umar ta yi watsi da karar da su Alhaji Bashir Tofa suka kai, inda suke neman kotun ta rusa sababbin masarautun guda biyar da Gwamnatin Jiha ta yi karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR.
Fiye da mutane dubu daya sun kamu da cutar covid-19 a kano
Babban Attorney na jihar Kano wato Barrister Ibrahim Mukhtar ne ya kalubalanci karar akan cancantar masu karar akan neman a soke masarautun.
Kotun ta kara da cewa karar zata iya bude wani sabon shafi na kalubale kala kala aduk wani mataki da aka dauka akan masarautun nan gaba.
Don haka kotun tai watsi sa wannan kara kuma masarautun 5 suna nan daram.
No comments:
Post a Comment