El-Rufai ya sassauta dokar kulle, bayan gar kame jihar na tsawon kwanaki 75 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, June 9, 2020

El-Rufai ya sassauta dokar kulle, bayan gar kame jihar na tsawon kwanaki 75

El-Rufai ya sassauta dokar kulle, bayan gar kame jihar na tsawon kwanaki 75

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i ya sassauta dokar hana walwala da ya kafa a jihar Kaduna.

- Ya bayyana cewa, masallatan Juma'a, majami'u, manyan shaguna duk za su iya budewa amma tare da kiyaye dokokin.

- Ya shawarci jama'ar jihar da su bada goyon baya wurin dakile yaduwar cutar duk da sassaucin da aka samu.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i ya sassauta tsauraran dokokin da ya kafa don dakile annobar korona a jihar.

Kamar yadda gwamnan ya sanar a yau Talata, 9 ga watan Yunin 2020, ya ce manyan shaguna za su iya komawa bakin sana'o'insu.

Masallatan Juma'a da Majami'u za su iya budewa a ranakun Juma'a da Lahadi kadai, amma karkashin kiyaye dokoki.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa, masu sana'ar aski da wuraren wanke kai duk za su iya budewa.

Otal za su iya budewa tare da wuraren cin abinci da kuma mashaya. 

Wuraren cin abincin za su iya budewa ne bayan an yi musu feshin kashe kwayoyin cuta.

Haka zalika, Gwamnan ya bayyana cewa babu yi wuwar bude makarantu da kasuwanni.  

"Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samun matsaya a kan lokacin da ya kamata a bude kasuwanni ka makarantu," yace.

"Shugaban ma'aikatan jihar zai sanar da lokacin da ya kamata ma'aikata su koma bakin aikinsu," gwamnan ya kara da cewa.

Gwamna Nasir El-Rufai ya shawarci jama'ar jihar dasu bada goyon baya wajen dakile yaduwar annobar a jihar.

"Kamar yadda muka jure dokar hana walwala na kwanaki 75, mu koma neman na kanmu ba tare da taimakawa yaduwar cutar ba.

"Mu nuna cewa za mu iya zama lafiya duk da sassaucin dokar," El-Rufai yace.

Kwanaki 75 kenan da gwamnan ya sanar da rufe jihar tare da saka dokar hana walwala a cikinta tun bayan da ya kamu da muguwar annobar korona.

Dokar dai ta hada da rufe kasuwanni, majami'u, masallatan Juma'a da na sallolin farilla biyar, shaguna da sauransu.

No comments:

Post a Comment