Kwamitin yaki da cutar COVID-19 na shugaban kasa, Presidential Taks Force (PTF) sun ce akwai yiwuwar yanzu ne annobar cutar korona ta fara yaduwa a Najeriya.
PTF sun koka kan yadda yan Najeriya suke gudun zuwa yin gwajin wadda hakan yasa har yanzu mutane kalilan aka yi wa gwajin idan aka kwatanta da adadin mutanen da ke kasar.
Ban yarda da cutar korona ba, kuma baza ta kamani ba -Hon. Gudaji Kazaure
Sun sanar da hakan ne yayin da mambobin Kwamitin PTF suka bayyana a gaban kwamitin hadaka na majalisar wakilai da dattijai domin yi musu bayani kan yadda aka kashe kudaden da aka bawa Najeriya tallafi don yaki da corona.
Shugaban Kwamitin PTF, kuma sakataren gwmanatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana fargabansa kan rashin sanin yadda annobar za ta kasance inda ya roki 'yan majalisar su taimaka wurin wayar da Kan mutane a mazabansu.
Ya ce, "Wannan kwayar cutar na da hatsari sosai.
Har yanzu ba mu tsira ba, ya zama dole mu yi shiri.
Yan bindiga na kashe mutane Arana daya fiye da yawan da Korona ta kashe Tunda ta shiho
Ba mu san lokacin da cutar za ta tafi ba, hakan yasa ba mu kashe dukkan kudaden da aka bamu ba.
"Ba mu san tsawon lokacin da zamu magance cutar ba.
Ko kasafin kudin da shugaban yaki da annobar na kasa ya bayar na watanni shida ne.
Amma da izinin Allah za muyi nasara.
"Babu magani ko riga kafi.
Lamarin ya jefa mutane cikin damuwa. Komai ya rikice.
Yau gashi duk mun saka takunkumi. Ba haka muka saba ba.
"Akwai taimakon da za ku iya mana.
Akwai dokoki da za a iya yi saboda gaba.
Muna yaki da cutar a yanzu, bai dace mu bari wata annobar ta zo ba mu shirya ba. Ya zama dole muyi shiri."
Da fari, shugaban NCDC, Ihekweazu ya karyata jita jitar da ake yadawa na cewa hukumarsa ta kashe miliyoyin naira wurin aike wa da sakon kar ta kwana na wayar da kan 'yan Najeriya.
Ya ce, "Labarin sakonnin sakon tes karya ne. Ba zai yiwu mu kashe irin wannan kudin ba. Hasali ma, dukkan sakon da aka aike wa kowa kyauta ne daga kamfanonin sadarwa a kasar.
"Ba mu biya ko sisi ba domin sakon kar ta kwana.
A halin yanzu mutanen da muka yi wa gwaji ba su kai 100,000 ba. Al halin yanzu muna da kayan aikin yi wa mutum fiye da 200,000 gwaji."
No comments:
Post a Comment