Jami’an tsaro sun kama mutumin da yake yiwa jarirai ‘yan wata 3 fyade - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Wednesday, June 24, 2020

Jami’an tsaro sun kama mutumin da yake yiwa jarirai ‘yan wata 3 fyade

Jami’an tsaro sun kama mutumin da yake  yiwa jarirai ‘yan wata 3 fyade 

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa jami’an hukumar NSCDC sun cafke wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa, Ahmadu Yaro, wanda ake zargi da yiwa  jarirai fyade.

Wannan abu ya faru ne a wani kauye da ake kira Adogi, a karamar hukumar Lafia, jihar Nasarawa. A cikin wata guda, an yi wa kananan yara har shida fyade a kauyen Adogi.

Idan ba ku manta ba a ranar 27 ga watan Mayu, aka samu labarin cewa an yi wa wata karamar yarinya mai suna Rukayya Aliyu fyade. Wannan jaririya ba ta wuce kwanaki 90 a Duniya ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi yunkurin yin irin wannan lalata da wata jaririya mai watanni biyu da haihuwa. An kai wannan hari ne jim kadan bayan an yi lalata da Rukayya Aliyu.

An fahimci a kan yi amfani da irin wadannan kananan yara ne wadanda ba su wuce watanni uku zuwa shida da zuwa Duniya ba. Daga nan kuma a jefar dasu a kusa da wata makaranta.

Ana zargin cewa masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da-dama suna zama a wannan kauye. Haka zalika akwai malaman tsibbu da suka shahara a jihar da suke zaune a garin na Adogi.

Binciken da jaridar tayi, ya bayyana mata cewa akwai wasu miyagu a kauyen, dake yi wa irin wadannan mutane da suka saba yin mummunan fyade, farautar jariran da za ayi amfani dasu.

Babban jami’in NSCDC na jihar Nasarawa, Gidado Fari, ya ce za a gurfanar da Ahmadu Yaro a gaban kotu. Za a yi wannan ne da zarar an kammala binciken da ake yi a kan matashin.

Gidado Fari ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Laraba cewa Yaro ya amsa laifinsa, tare da bayyanawa jami’an tsaro yadda ya yi wa wasu kananan yara biyar 5 irin wannan danyen aiki.

Fari ya ce wanda ake zargin ya na ikirarin cewa ya na fama da tabin hankali, abin da ba a iya tabbatarwa ba tukunna. Ana zargin shi kadai ne, yake addabar mutanen kauyen da fyade.

No comments:

Post a Comment