Obasanjo ya yi gargadi kan da matsalar karancin abinci da za a fuskanta bayan cutar korona ta wuce. - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, June 9, 2020

Obasanjo ya yi gargadi kan da matsalar karancin abinci da za a fuskanta bayan cutar korona ta wuce.

Obasanjo ya yi gargadi kan da matsalar karancin abinci da za a fuskanta bayan cutar korona ta wuce.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi gargadi game da matsalar karancin abinci da za a fuskanta a Najeriya da sauran kasashen nahiyyar Afirka bayan annobar cutar korona ta gushe.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Obasanjo ya bukaci gwamnatocin kasashen da su tashi tsaye wajen fuskantar kalubalen dake ci gaba da tunkaro su.

Tsohon shugaban kasar ya nemi ‘yan Najeriya da su dauki batun abin da zai faru bayan gushewar annobar korona da mahimmancin gaske.

Yana mai cewa, bayan likafar annobar korona ta gama cin kasuwarta, za kuma ta bude kofar matsalar karancin abinci a Nahiyar Afirka.

Dattijon ya fadi hakan ne a harabar Laburarensa na Olusegun Obasanjo Presidential Library dake birnin Abeokuta a jihar Ogun.

Furucin tsohon shugaban kasar ya zo ne yayin da ya kaddamar da shirin fara aikin noman kifi, a karshen mako da ya gabata.

Haka kuma Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar da ke kula da kasuwanci ta duniya, WTO sun yi irin wannan gargadi na tsohon shugaban Najeriya Obasanjo.

Sun yi kashedin cewa akwai yiwuwar duniya za ta fuskanci karancin abinci idan mahukunta suka gaza shawo kan annobar korona.

Hukumomin biyu sun ce dokar kulle da gwamnatoci a duniya suka sanya ta yi mummunar takaita hada-hadar kayan abinci a kasuwannin duniya.

Haka zalika dokar kulle da aka shimfida a kasashen duniya saboda takaita yaduwar cutar korona, ta kara haifar da karanci da tsadar abinci a wasu wurare.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutum 315 da suka kamu da cutar korona a Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya ta fitar da misalin karfe 11.41 na daren ranar Litinin 8 ga Yuni na shekarar 2020.

Alkalluman da Hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa, jimillar wadanda suka kamu da cutar korona a kasar ya kai dubu goma sha biyu da dari takwas da daya 12,801.

No comments:

Post a Comment