Ayau Talata ne mazauna garin Yan tumaki a karamar hukumar Dan musa a jihar Katsina suka yi tururuwar fitowa kan tituna domin gudanar da zanga - zanga a kan halin rashin tsaro da suke fama dashi.
Zanga - zangar ta barke ne sakamakon sace wani ma'aikacin lafiya da diyarsa da wasu 'yan bindiga sukayi.
Wata majiya ta shaidawa jaridar Premium Times cewa wasu 'yan bindiga ne suka kaiwa ma'aikacin lafiyar, Mansir Yusuf, hari da misalin karfe 1:00 na dare tare da yin awon gaba dashi da diyarsa.
Garkuwa da ma'aikacin lafiyar da diyarsa na zuwa ne a cikin kasa da mako biyu da kai hari tare da kashe hakimin Yan tumaki, Atiku Abubakar, wanda 'yan bindiga suka harbe a gidansa.
Jami'an tsaron Najeriya ba sa yin abinda yakamata Kan yaki da Yan bindiga- Gudaji Kazaure https://youtu.be/EVauMKSVUq4
Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta sanar da Premium Times cewa ma'aikacin lafiyar da aka sace makwabci ne ga hakimin da 'yan bindiga suka kashe.
Masu zanga - zangar, yawancinsu matasane, da kananan yara, sun rufe manyan hanyoyi, tare da sukar gwamnati a kan nuna halin 'ko in kula' tun bayan kisan hakimin garin.
"Har yanzu babu wani jami'in tsaro a garin tun bayan kisan hakimi.
Sun ce suna yin zanga - zanga ne domin jan hankalin gwamnati kafin wadannan 'yan bindigar su fara kawo musua hari a kowace rana.
No comments:
Post a Comment