Mayakan ta'addancin sun tsinkayi garin Monguno wurin karfe 11:30 inda suke ta harbe-harbe ta ko ina.
Kamar yadda majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar, ana musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da dakarun sojin Najeriya.
Ma'aikacin NGO ya sanar da jaridar Daily Trust cewa harbe- harben bindiga da kararta ne yake ta tashi ta ko ina.
"A halin yanzu da muke magana, mayakan suna nan a Monguno, ana ta jin tashin karar bindiga.
Yace: Dakarun soji na ragar-gazarsu. Ba mu da kwanciyar hankali.
Haka zalika, 'yan ta'adddan sun kai hari a wani kauye mai suna Usmanati Goni dake karamar hukumar Nganzai a sa'o'in farko na ranar Asabar.
Kamar yadda wani mafarauci ya sanar, maharan sun bayyana wurin karfe 10 na safe inda suka fara harbin farar hula.
Har a halin yanzu ba a san yawan jama'ar da aka kashe ba a yayin rubuta wannan rahoton.
Rundunar sojin Najeriya ta fatattaki mayakan ISWAP a garin Monguno da ke jihar Borno ta yankin arewa maso gabas din kasar nan.
Jami'an tsaro da mayakan sun yi musayar wuta bayan da 'yan ta'addan suka kutsa garin a ranar Asabar tare da fara harbe-harbe.
Dubban 'yan gudun hijira da ke garin sun fara tserewa don neman mafaka.
Channels TV ta gano cewa, mayakan sun kai hari garin Nganzai da Gubio a lokaci daya duk da ba a samu rashin rayuka ba.
No comments:
Post a Comment