Ina son naje yi wa jama'a jaje amma ina gudun muje ace mana karya ne - Masari
A wani taron manema labarai da gwamnan jihar Katsina Rt Hon Aminu Bello Masari ya fitar game da yawan kai hare-haren ta'addanci da yan bindiga ke yi a jihar Katsina, gwamnan ya bayyana cewa a jihar Katsina barnar da yan ta'adda suke yi a jihar ta fi ta coronavirus illa matuka a jihar.
Gwamnan ya ce a cikin kwana daya ya lissafa yan bindiga sun kashe masa sama da mutum 51 sakamakon harin yan ta'addan.
Gwamnan ya kuma bayyana dalilinsa na dakatar da zuwa jajen wandada aka kashe a garuruwansu, sakamakon ya je ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, kuma duk inda ya je yakan tabbatar wa al'ummar yankin cewa insha Allah abin ya zo karshe, bayan nan kuma barayin sukan sake komawa suyi ta'addanci a garin, inda yace to in ya koma yin ja je da wace magana zai tunkari al'ummar yankin? Illa sai ma suce karya ce kawai yake sharo masu, domin andade ana ruwa kasa na shanyewa, kamar yadda gwamnan yayi ikirari a cikin jawabinsa.
Za a iya tuna cewa ko a lokacin da wasu mahara suka kai mummunan hari a Kadisau karamar hukumar Faskari, Katsina Daily Post News ta rawaito cewa Gwamnan jihar Katsina bai leka karamar hukumar don yi musu jaje ba.
Ko a hudumar limanin Jumu'a na Masallacin JIBWIS cikin garin Katsina Liman Malam Husamatu ya bayyana takaicinsa, na zargin gwamnatin tarayya da sakaci wajen halin ko'inkula da yadda ake ta kai hare-hare a yankunan Batsari Faskari Sabuwa da sauransu a jihar Katsina, inda yace yadda aka dauki matakai a kan cutar coronavirus a jihar da haka aka dauka a kan matsalar tsaro a jihar da tuni abin ya zama tarihi.
No comments:
Post a Comment