An kori jami'in kwastam da Buhari ya karrama saboda ƙin karɓar toshiyar bakin Naira miliyan 180
- Hukumar Kwastam ta kori jamiinta da ya yi fice wurin yaki da cin hanci da rashawa, Bashir Abubakar
- Ta kuma sallami wani jami'inta mai mukamakin mataimakin shugaba mai suna Aminu Dahiru
- Sanarwar da Kakakin hukumar ya fitar ta ce an kore su daga aiki ne bayan samunsu da sakaci
Hukumar Hana Fasakwabri, Kwastam, a ranar Laraba ta sanar da korar jami’inta, mataimakin shugaba (ACG) Aminu Dahiru da kuma tilasta wa wani jami’in, ACG Bashir Abubakar yin murabus.
ACG Bashir Abubakar dai shine jami'in da Shugaba Muhammadu Buhari ya karrama da lambar girmamawa shekarar 2019 saboda kin karbar toshiyar baki na Dalar Amurka 412,000 kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Sanarwar da kakakin hukumar, Joseph Attah ya fitar a madadin Shugabanta, Hamid Ali ta ce mambobin kwamitin zartarwa na hukumar sun amince da wannan matakin da ya dace da tsarin yi wa hukumar garambawul.
An kori jami'an biyu, Abubakar da Dahiru ne bayan samun su da laifin sakaci a watan da ya gabata kamar yadda binciken da kwamitin ladabtarwa da aka kafa ya bayyana.
An tuhumi ACG Aminu Dahiru da hannu a badakalar fasakwabrin manyan motoci guda 295 dauke da man fetur a watan Disambar 2019 lokacin yana aiki da Rundunar Kare kan Iyakokin kan Tudu na Kasa.
DUBA WANNAN:
Shi kuma ACG Bashir Abubakar ana zarginsa da bayar da umarnin yin sumame a rumbun ajiyar shinkafa ‘yar gida a kokarinsa na gano shinkafar waje a rumbunan ajiyar wani fitaccen mutum a garin Daura da ke Jihar Katsina.
A watan Nuwamban 2019, Shugaba Buhari da Shugaban Hukumar Kwastam, Hamid Ali suka karrama Bashir Abubakar da lambar yabo bisa gaskiyarsa da jajircewa wurin aiki.
Bashir Abubakar ya kuma samu yabo daga hukumar a shekarar 2018 bayan da yaƙi karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 412,000 daga hannun wasu da suka shigo da haramtattun kwayoyin Tramadol lokacin yana kula da rundunar a shiyar Apapa a Legas, lamarin da yasa yayi fice.
Har wa yau, Sanarwar ta ce rundunar ta yi wa wasu jamianta 2,634 karin girma tare da tabbatar da naɗin masu taimakawa shugaban rundunar guda biyar.
Magu ya fallasa Yadda Malami ya karya doka, yayi gwanjon kayan satar da EFCC ta kama
No comments:
Post a Comment