An sako dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu bayan ya shefe kwana 10 a tsare yana fusknatar bincike.
A ranar Litinin 6 ga watan Yuli ne Jami’an tsaro na DSS suka kai Magu gaban kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa domin binciken zarge-zargen da ake masa guda 12 kan jagorancinsa a EFCC.
Tuhume-tuhumen sun hada da kasa bayar da bayani kan kudin ruwan da aka samu a kan kuÉ—i Naira biliyan 550 da aka kwato daga wasu barayin dukiyar gwamnati.
Yana fuskantar bincike ne a gaban kwamitin tsohon Mai Shari’a Ayo Salama, lamarin da ya sa aka dakatar da shi tare da daukacin darektoci da wasu manyan jami’an gudanarwan hukumar.
No comments:
Post a Comment