Za A Riƙa Dandaƙe Masu Fyaɗe A Kano
Majalisar dokokin jihar Kano sun kaddamar da shirye-shiryen sauya dokar jihar ta Penal Code (No.12), domin tabbatar da an dandaƙe duk wanda aka kama da laifin fyaɗe a jihar.
Membobin majalisar sunyi muhawara kan hakan ne sakamakon kudirin da memba Nurudeen Alhassan mai wakiltar mazabar Rano ya shigar da bukatar sauya dokar.
An ruwaito cewa Kakakin majalisar, AbdulAzeez Gafasa, da sauran yan majalisan sun yi ittifaki kan lallai mai fyade ya cancanci hukuncin dandatsa.
Alhassan Ya ce; Ina kira ga majalisa ta sake duba wannan dokar a sauya ta, domin samar da hukuncin dandatsa kan masu fyade.
An kashe mijimmu an bar mana marayu 15 a Batsari
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-kashe-maigidanmu-bar-mana-marayu-15.html
An kashe mijimmu an bar mana marayu 15 a Batsari
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-kashe-maigidanmu-bar-mana-marayu-15.html
Na yi imanin cewa wannan kadai shine matakin da za a iya dauka domin kawo karshen fyade cikin al’umma saboda ya zama ruwan dare.
” Ya kara da cewa idan iyaye za su iya daina daurawa yaransu talla, da hakan zai taimaka matuka wajen kawo karshen annobar.
Ya ce yawancin masu aikata laifin na amfani da yan talla musamman a wuraren da ake aikin gine-gine.
No comments:
Post a Comment