A wata takarda da Garba Shehu, Mai magana da yawun shugaban kasa yafitar, ya yi bayanin dalilin da yasa Buhari ya aminta da dakatar da Magu.
"An sami korafi daban-daban a kan mukaddashin shugaban hukumar EFCC.
Bayan bincike na farko, an kira jami'an da ke karkashinsa inda aka bincikesu.
"A saboda haka aka kafa kwamitin bincike mai kiyaye dokokin hukumar.
"A duk lokacin da ake zargin shugaban wata hukuma, akan buƙacesa da ya dakata da aiki, don a samu damar yin bincike ba tare da wata matsala ba.
"EFCC bata dogaro da yanayin mutum, a don haka bata sassauta wa kowa.
An bankaÉ—o Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai
Dakatar da Magu kuwa ya bai wa hukumar damar sauke nauyinta ba tare da wani cikas ba.
"EFCC na da zaƙa-ƙurai, jajirtattun ma'aikata maza da mata masu fatan kiyaye dukkan dokokin ƙasar nan, tare da mika duk wanda yazo da almundahana gaban hukuma.
"Amma kuma, an bai wa Magu damar da zai kare kansa tare da amsa tambayoyin da ake masa.
Hakan ce kuwa ta kamata a karkashin dokar kasar nan wacce ta bai wa kowa damar kare kansa," takardar tace.
Garba Shehu ya kara da cewa, dole ne a gane cewa yaki da rashawa a kasar nan ba a wuri daya ake tsayawa ba. Ta kowanne fanni ana kokarin tabbatar da shi.
Mu Magance Cin Hanci da Rashawa a Afrika
No comments:
Post a Comment