Mu yaƙi Cin Hanci da Rashawa a Afrika - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Sunday, July 12, 2020

Mu yaƙi Cin Hanci da Rashawa a Afrika

Shugaba  Muhammadu Buhari, a jiya, ya ce  cin hanci da rashawa yana haifar da rashin shugabanci a Afirka.

Buhari ya ce irin wannan mummunar ci gaba ya haifar da mummunan sakamako wanda ya dagula yanayin tattalin arziki da siyasa a Afirka.

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, yayin da nahiyar ke bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa, ranar 11 ga watan Yuli, 2020, Shugaban ya roki shugabannin Afirka da su tabbatar da aiwatar da Matsayi na Afirka akan kula da tattalin arzikin kasa  (CAPAR)

Kwamitin Shugaban ƙasa ya ban kaɗo Naira Bilyan 5,50 da EFCC ta ƙwato 

Shugaban, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya nemi a sake tabbatar da  yakin cin hanci da rashawa da shugabannin Afirka ke yi don samar da “Afirka mai cike da wadata da kwanciyar hankali.

Ya yi takaicin cewa “cin hanci da rashawa da ake aikatawar a duk jihohinmu na kasa sun haifar da rashin kyakkyawan shugabanci wanda hakan ya haifar da munanan sakamako wanda ya kara dagula yanayin tattalin arziki da siyasa a Afirka.”

 An bankaɗo Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai

No comments:

Post a Comment