ƊAUKI NAUYIN ƊALIBAI 60 DOMIN KARATUN LIKITA A KASAR WAJE
Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa ya umarchi ma'aikatar Lafiya ƙarƙashin kwaminshinan Lafiya Dr. Abba Zakari Umar da su tantance yara 60 ƴan asalin jihar Jigawa masu sha'awar karatun likita wato medicine domin gwamnati ta ɗauki nauyin su zuwa karatu kasar waje.
Za'a ɗauki yara biyu daga kowace mazaɓar dan majalissa.
Ana bukatar yara ƴan ƙasa da shekaru 23, waɗanda suke da a ƙalla credit 5 a Biology, Chemistry, Physics, English da mathematics.
Wannan shiri na ƴa ƴan talakawa ne kawai waɗanda suka gama karatun secondary a makarantun gwamnati kuma za'a zaƙulo yaran bisa chancanta kawai.
Ana bukatar ɗaukar a ƙalla mata 30, maza 30.
Duk me sha'awa yakai takardunsa ofishin kwamishinan lafiya na Jigawa Dr. Abba Zakari Umar daga Juma'a 3rd July.
Za'a rufe karɓar takardun ranar 10 ga July kuma ayi jarrabawa ranar litinin 13th July 2020.
No comments:
Post a Comment