Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta ce za ta gudanar da zanga-zanga don nuna adawarta da ƙarin farashin naira 20 kan duk litar man fetur ɗaya a ƙasar.
Ƙungiyar ta ce ƙarin farashin man a wannan lokaci, "bai dace ba.... son kai da son zuciya ne ya sa aka yi maza aka yi, don wasu mutane su samu ribar da ba ta kan ƙa'ida."
Da yake zantawa da BBC, shugaban ƙwadago na Najeriya, Kwamared Ayuba Wabba ya yi zargin cewa a bayanan sun samu labarin akwai man fetur jibge cikin jiragen ruwa da kuma wanda ke ƙasa fiye da lita biliyan ɗaya, kuma an sayi duk lita ne a kan N107.
Jaridar Premium Times ta ambato Babban Sakataren hukumar ƙayyade farashin albarkatun man fetur, Saidu Abdulkadir, na cewa sun yi la'akari da zahirin kuɗin aikace-aikace da dillalan mai ke kashewa" gabanin sanar da sabon farashin.
Ya ce farashin sayar da man fetur a cikin watan Yulin 2020 da suka ba da shawara zai kama daga N140.80 zuwa N143.80 a kan kowacce lita. Sabon farashin dai ya maye gurbin wanda hukumar ta sanar na N121.50 zuwa N123.50 a cikin watan jiya.
Jami'in ya ce sun cimma matsaya kan farashin da ake ba da shawarar ne bayan yin bita kan harkokin kasuwar ɗanyen man fetur ta watan Yuni.
Sai dai shugaban ƙwadagon ya ce ya tuntuɓi mutane da yawa ciki har da masu shigar da man fetur Najeriya, kuma sun shaida masa cewa "akwai son rai cikin ƙarin" farashin.
Ayuba Wabba ya kuma bayyana damuwar cewa ƙarin na zuwa ne kwana biyu kacal da ɗage matakan hana zirga-zirga tsakanin jihohin ƙasar "domin ma mutane su samu gajiyar ragin da aka yi a watan jiya".
Amma kuma kwatsam sai aka ƙara daga N123 zuwa N143, in ji jagoran 'yan ƙwadagon Najeriya.
"Gaskiya ba mu amince da wannan ba. Kuma 'yan Najeriya ma ba su amince da shi ba, saboda babu adalci a ciki".
A cewarsa ƙarin da aka yi ba ya kan ƙa'ida. "Duk wani bayani da PPPRA (hukumar ƙayyade farashin man fetur ta Najeriya) suka yi, mun bincika, mun gano bayanin ba haka yake ba"
Ya yi zargin cewa hukumomin ƙasar sun yi ƙarin farashin man ne ba tare da bayar da sanarwa ko notis ba.
Idan ka duba, wanda ya saya a kan N107 kamar yadda ake sayarwa dillalai, waɗanda suke da kaya a bayanan da muka samu, ya fi lita miliyan ɗari biyar, a cewar Ayuba Wabba.
Ya ce an yi ƙarin gwauron zabbin ne don amfanin wasu mutane ƙalilan.
'Me ya sa ba za mu iya tace man nan domin a taimaka wa 'yan Najeriya, kamar yadda wasu ƙasashe masu arziƙin man fetur suke yi ba?" Wabba ya tambaya.
Ya ce za su yi zanga-zangar lumana kamar yadda tsarin mulkin ƙasa ya ba su dama, don nuna rashin amincewarsu ga wannan mataki a ƙasar.
"Insha Allahu, idan na kira mitin na ƙasa gaba ɗaya ranar 15 ga wannan wata, a lokacin ne za a yanke hukunci kan abin da ya kamata a yi."
No comments:
Post a Comment