- An ɓullo da Wasu sabbin tuhume-tuhume kan shugaban EFCC da aka dakatar
- Sifeto Janar na yan sanda ya janye dukkan jami'ansa dake gadin ofishin EFCC da Magu
Lauyan muƙaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa wato EFCC Ibrahim Magu wanda aka dakatar, a ranar Juma'a ya bukaci kwamitin fadar shugaban kasa dake bincike a kansa a ba dashi beli.
Ya ce akwai bukatar sakin Magu saboda yan jarida na amfani da damar tsareshi da akayi wajen wallafe-wallafen ɓata masa suna.
Sannan Ya ƙara da wasu bukatu shida daban.
Magu ya ce kwamitin ya kira masu shaida kansa, amma ba'a bari ya gansu ba, balle amsa laifinsa ko kin amsawa.
Lauyansa, Mista Wahab Shittu, ya bayyana hakan ranar 10 ga Yuli, 2020.
Atiku ya soki gwamnatin Najeriya kan dakatar da jarrabawar WAEC
Ga jerin bukatu 7 da ya mikawa kwamitin:
Wahab Shittu yace: "Bisa bayanan da mukayi, muna masu buƙatar wadannan abubuwa a wurinka ya mai girma mai shari;a, da sauran mambobin kwamitin:
1. A baiwa Magu damar ganin manufar wannan kwamiti da abinda take niyyar yi
2. A nunawa Magu takardun tuhume-tuhumen da ake yi masa domin bashi daman ganinsu, karantasu tare da shiryawa martani ko kare kansa.
3. Magu na bukatar taimakon wannan kwamiti domin a sakeshi daga hannun hukuma domin ya sami damar kare kansa sosai da kuma kula da lafiyarsa da ya fara samun matsala a tsare.
4. A baiwa Magu isasshen lokaci, yayi bayani kan tuhume-tuhumen da ake yi masa tare da gabatar da hujjoji ga kwamitin.
5. A baiwa Magu damar gaba da gaba da wadanda suka shigar da kara a kansa da hujjojinsa.
6. Shaid: su gabatar da shaidarsu a gabansa
7. A baiwa Magu daman amsa laifinsa cikin tsanaki tare da hakkinsa na yanci yayin aikin wannan kwamiti
"Ya mai girma mai shari'a, shugaban kwamiti da mambobi, abokinmu zai yi matukar godiya idan kuka dau matakin wuri kan wadannan bukatu da ya mika a wasikar nan."
No comments:
Post a Comment