Mutane Milyan 4.48 Sun Nemi Aikin N-Power cinkin kwanaki 16 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Tuesday, July 14, 2020

Mutane Milyan 4.48 Sun Nemi Aikin N-Power cinkin kwanaki 16

Gwamnatin Najeriya ta ce kusan mutune miliyan biyar ne suke son cin moriyar shirin samar da aikin yi ga matasa wanda aka fi sani da N-Power.

Ministar ma'aikatar bayar da agaji da ayyukan gaggawa Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan a shafinta na Twitter.

"Kwanaki 16 ke nan tun da aka bude shafin da ake karbar takardun neman aiki, kawo yanzu mun sami takardu miliyan 4.48", a cewar ministar a sakon da ta wallafa ranar 12 ga watan Yuli.

Ta kara da cewa ita da ma'aikatanta suna aiki tukuru wajen ganin shirin ya tafi kamar yadda ya kamata.

Ranar 26 ga watan Yunin 2020 aka bude shafin neman aikin na N-Power wanda za a ɗauki sati shida ana karɓar takardun neman aikin.

Anyi binciken Æ™wa-Æ™waf a Offishin Magu tare da awon Gaba da Na'urar Bayanai 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/an-binciken-wa-waf-offishin-magu-tare.html

 Ga yadda za kubi kuyi rijistar Shirin N-Power 2020

A wannan rukuni na C na watan Yunin 2020 masu neman aikin za suyi rijista ne ta intanet a
www.npower.fmhds.gov.ng website

Sannan ba kowa ne zai iya neman aikin ba, sai wadanda shekarunsu ke tsakanin 18 da 35.

Ga abubuwan da kuke bukata a hannun ku kafin ku nemi aikin:

Lambar tantance asusun ajiya na banki (BVN)

Karamin hoto da ake kira fasfo na jpeg ko PNG

Adireshin i-mail ko lambar wayar wajen aikin

Sakamakon digiri ko takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima

Gwamnatin Kano ta ware Bilyan 3 Domin yaÆ™ar cutar Maleriya 
https://www.arewagist.com.ng/2020/07/a-ranar-lahadin-da-ta-gabata-ne-gwamnan.html

Ga abin da ake bukatar ku yi da zarar kun shiga shafin intanet din yin rijistar :

Ku sanya bayanin inda za a same ku (adireshin i-mail da lambar waya) a bangaren da aka ware don yin hakan.

Bayanan da kuka sanya din zai kai ku cikin i-mail dinku don ku tabbatar da hakan.

Da zarar kun tabbatar da adireshin i-mail dinku, sai ku cike wajen da aka tanada don sanya lambobi 11 na tantance asusun ajiya na banki (BVN) sannan ku sanya ranar haihuwa ta hanyar farawa da ranar kwanan wata, sai watan haihuwar sa ikuma shekarar haihuwar taku (dd/mm/yr)

Shafin bayani a kanku da kuma na tuntubarku: ku sanya sunan kaka, sunanku na yanka da kuma sunan mahaifi, kamar yadda kuka Sanya lokacin da za kuyi rijistar lamabar tantance asusun ajiyarku na banki BVN.

Shafin bayani kan Ilimi da Shirin: a wannan bangaren za ku sanya matakin iliminku. An bude shirin na N-power ne ga kowa da kowa

Shirin N-Tech da N- health kuwa an bude su ne kawai ga masu shaidar kammala digiri.

Shirin N-Power na bangaren Lafiya na masu digiri da HND da OND ne kamar wadanda suka karanci aikin likita da aikin jinya da Ilimin Tsirrai da Unguwarzoma da Ilimin Sanin Hallayyar dan adam da Ilimin halittun da ido ba ya gani wato Microbiology.

Kuna bukatar sanya takardar shaidar digirin a komfuta don aikewa da shi a yayin yin rijistar.

Shafin bayani kan aikin da aka taba yi da kuma sauran bayanai: Za ku amsa wasu tambayoyi tare da sanya katin shaida.

 Ga dai katin shaidar da gwamnati ta yarda ku yi amfani da su a kasa:

Fasfo din tafiye-tafiye

Katin shaidar zama dan kasa da hukumar NIMC ta bayar

Ingantaccen lasisin tuka mota

Katin zabe na dindindin

Yara kusan miliyan 10 za su daina karatu har abada- Inji Save the Children

https://www.arewagist.com.ng/2020/07/yara-miliyan-97-za-su-daina-karatu.html


Shafin da za ku sake duba bayanan da kyau sannan ku aike

Ku duba bayanan da kuka cike duka sannan ku aike

Bayan kun aike za ku samu wata lamba ta musamman, sai ku dauke ta ku adana ta da kyau.


Hukumomi sun ce shirin zai dauki mutum 400,000 da za su yi aiki a bangarori da dama da suka hada da Noma da lafiya da koyarwa da gine-gine da fasaha

A shekarar 2016 ne gwamnati ta samar da shirin kuma zuwa yanzu an tallafa wa mutum 500,000

Domin Samun manyan labaran da Muke wallafawa ku biyo mu a
https://m.facebook.com/AREWAGIST.com.ng/?ref=bookmarks
https://mobile.twitter.com/ArewagistN

No comments:

Post a Comment