Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a kasar.
A baya dai ana yanke hukuncin daurin shekara 10 ga mutanen da aka kama da laifin.
Mutane Milyan 4.48 Sun Nemi Aikin N-Power cinkin kwanaki 16
Haka kuma majalisar ta soke bambanci jinsi maza ko mata kan laifin fyade inda ta bayyana cewa maza ma Ana iya Yi musu fyade.
Wannan matsaya da majalisar da cimma ta biyo bayan tsallake karatu na uku da kudurin ya yi tare da sauya dokar manyan laifuka ta kasar, ta 2004."
'Yar majalisa da ke wakiltar jihar Legas ta tsakiya Sanata Oluremi Tinubu ce ta nemi a kara tsaurara dokar da kuma cire banbanci a tsakanin jinsi a lokacin hukunci kan fyade.
Kudurin ya cire wa'adin gabatar da kara kan cin zarafi a kasar baki daya.
Idan kudurin ya zama doka, hukuncin cin zarafin zai zama za a iya aiki da shi a ko wanne lokaci.
No comments:
Post a Comment