Rundunar Ƴan sanda sun kama wani Francis Diamond da ake yi wa laƙabi da Iron Man, shugaban wata mugunyar kungiyar asiri ta Aiye a jihar Legas.
An kama Diamond ne bayan wasu hare hare da kisan kai da fashi da makami da aka yi a unguwanin Ajah da Epe a jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar ta Legas ta danganta laifukan da aka aikata da kungiyar asirin, wanda ake zargin.
Majalisar wakilai ta bukaci INEC ta dawo da Naira Bilyan 73
Yan sandan sun kuma kama wasu mambobin kungiyar takwas a sassa daban na Ikorodu bayan shugaban kungiyar ya bayyana musu inda suke.
An ce wadanda ake zargin sun kashe wani dan kungiyar da suke kishi a Odonguyan, Ikorodu kuma suka kai wa wasu mutane a yankin hari.
Ƴan sandan sun ce Diamond ya amsa cewa ya ɗauki faifan bidiyon lokacin da aka kashe ɗayan ɗan ƙungiyar da suke adawa ta adda.
Shugaban kungiyar ya ce, "Na daura bidiyon a intanet saboda kowa ya gani musamman 'yan kungiyarsa.
Shi ne ya tsara wani hari da aka kai wa dan kungiyar mu.
Ɗaliban Najeriya bazasu rubuta jarabawar WAEC ta 2020 ba
" Kakakin rundunar yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya bayar da sunayen 'yan kungiyar da aka kama kamar haka;
Olaitan Apampa; Chidi Michael, 25; Eno Sunday, 25; Saheed Gbadebo, 23; Adepeju Azeez, 38; Samuel Ilesanmi; Omotosho Quadri, 25, da Moses Ogungbe, 28.
Elkana ya ce binciken da yan sanda suka gudanar ya nuna cewa Apampa ne ya harbi wanda suke kashe bayan sun gama sararsa da adda.
Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce, "Wadanda ake zargi yan kungiyar asiri ta Eiye ne.
Sun ce sun kashe matashin da suka kashe ne saboda yana da hannu wurin kashe daya daga cikin shugaban su a jami'ar Ibadan a farkon wannan shekarar.
"An kuma gano cewa wadanda ake zargin sun saba kashe mutane musamman yan kungiyar da suke adawa da su a Ikorodu da kewaye.
Majalisar dattawa ta maida wa'adin Sifeton Yan sanda shekara 4
Saheed Gbadebo shi kadai ya kashe mutum biyu a Bayekun Street, Ikorodu, da mutum biyar a Ajah.
"Za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike."
No comments:
Post a Comment