Bankin Duniya zai bai wa Najeriya naira biliyan 43 - Arewagist.com.ng

Breaking

Arewagist.com.ng

Sayi DATA Ta MTN 1Gig 350, 2Gig 700 3Gig 1k 5Gig 1500 WhatsApp 08122225296

Saturday, August 8, 2020

Bankin Duniya zai bai wa Najeriya naira biliyan 43

 

Bankin Duniya zai bai wa Najeriya naira biliyan 43

Bankin Duniya ya amince ya bai wa Najeriya tallafin dala miliyan 114.28 - kwatankwacin naira biliyan 43 - domin yaƙi da annobar korona musamman a matakin jihohi, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.


A cewar wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a, dala miliyan 100 za ta fito ne daga ƙungiyar International Development Association (IDA), sai kuma miliyan 14.28 da za ta fito daga sashen Pandemic Emergency Financing Facility.


Ta ce Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta bayar da lamuni ga jihohi 36 na ƙasar ciki har da Abuja ta hanyar tsarin yaƙi da annobar da aka yi wa laƙabi da COVID-19 Preparedness and Response Project (CoPREP).


Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka matuƙa a matsayin ɗaukin gaggawa da zai daƙile bazuwar cutar a tsakanin al'umma.


Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Mista Shubham Chaudhuri ya ce: "Najeriya ta duƙufa wurin daƙile yaɗuwar annobar korona, sai dai akwai buƙatar a ƙara ƙaimi sosai musamman a matakin jihohi, waɗanda su ne kan gaba a yaƙi da cutar.


"Shirin zai taimaka wa jihohi da abin da suka fi buƙata na kayan aiki da kuɗi domin ƙarfafa gwiwarsu wurin yaƙi da annobar."

Mutum 45,687 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya, 936 daga cikinsu sun mutu sannan 32,637 sun warke.


No comments:

Post a Comment