Bankin CBN ya kashe N 75b wajen buga kudi a shekarar 2019
Babban bankin Najeriya CBN ya ce ya kashe bilyan 75 wajen buga kudade a shekarar 2019 kadai. Karin bilyan 11.5 kan abinda aka kashe a shekarar 2018, akan biyan N 64b.
Babban bankin ya kara da cewa an baiwa yan kasuwar canji da hukumomin Hajji da Umrah $3.95 billion, kuma a matsayin alawus na tafiye-tafiye ga ma'aikatun gwamnati a shekarar.
Bayan haka, CBN ta bayyana cewa an samu ragin milyan N365.5 na kudin da mutane ke ajiyew a banki.
Dukka wannan ya bayyana ne a rahoton shekara-shekara da bankin ya saki na shekarar 2019, Wanda Vanguard ta ruwaito.
Rahoton yace: "Jimillan kudin da aka kashe wajen buga takardun kudi a 2019 shine N75.5 billion, sabanin N64 billion a 2018, hakan na nuna cewa an samu karin bilyan 11.5."
"An sayi kudin dala $3.95 billion a 2019, yayinda aka tura $2.58 billion jihar Legas, an bada $1.38bn ga Abuja da sauran jihohi."
https://www.thedigitaldollar.io/bundles/thedigitaldollar/assets/images/referral_banner/46860.gif
"An yi amfani da kudin ne wajen baiwa yan kasuwar canji da hukumomin Hajji, hakazalika wajen biyan kudin alawus na tafiye-tafiye ga ministoci, da manyan jami'an gwamnati."
A bangare guda, Dirakta Manaja na kamfanin Financial Derivatives, Bismarck Rewane, ya ce tattalin arzikin Najeriya zai durkushe nan da watanni masu zuwa a rubi'in kusa da karshen shekarar 2020.
Rewane ya bayyana hakan ga wakilan The Punch a ranar Talata inda yayi tsokaci kan Alkaluman da hukumar lissafin Najeriya NBS ta saki kan yanayin tattalin arzikin Najeriya.
Rewane ya ce durkushewar tattalin arzikin Najeriya na nufin cewa za'a samu karuwan rashin aiki yi.
Bayan haka, ya kara da cewa za'a ga yawan mutanen da zasu fada bakin talauci saboda karancin kudin da rashin aikin yi.
Wednesday, August 26, 2020
New
Bankin CBN ya kashe N 75b wajen buga kudi a shekarar 2019
About Bahaushiyanews.com
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
Tattalin Arziki
Tags
Labarai,
Tattalin Arziki
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment