Kaduna ta dakatar da masu Keke-Napep aiki a babban titin da ya ratsa jihar
Ma’aikatar Sufuri ta jihar Kaduna ta dakatar da masu aikin haya da Keke Napep aiki a babban titin da ya ratsa Kaduna tundaga Kawo har Mahadar Kwamand.
Wannan sanarwa ta fito daga ofishin ma’aikatar Sufuri ta jihar ne wadda shugabar hukumar Aisha Said-Bala ta saka wa hannu.
Sannan kuma hukumar ta ce Æ´an dokan jihar, wato KASTELEA za su bazu ta ko-ina a jihar domin tabbatar da masu Keke Napep sun bi wannan umarni da doka.
Bayan haka kuma, hukumar ta umarci masu motocin haya su garzaya hukumar domin sabunta rajistar motocinsu wanda za a fara dada 30 ga Agusta zuwa 30 ga Satumba.
Masu Keke-Napep a jihar sun koka matuka game da wannan sabon doka.
Wani matuki ya ce yanzu ya zama kenan kowa zai yi aiki ne a unguwar sa. Babu ketarawa wani unguwa ba.
Saturday, August 29, 2020
New
Kaduna ta dakatar da masu Keke-Napep aiki a babban titin da ya ratsa jihar
About Bahaushiyanews.com
SoraTemplates is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of SoraTemplates is to provide the best quality blogger templates.
Labarai
Tags
Labarai
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment